Jiragen Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan Ƴan Ta'adda, an Kashe Miyagu 40

Jiragen Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan Ƴan Ta'adda, an Kashe Miyagu 40

  • Hare-haren jiragen yakin sojojin Najeriya sun hallaka mayakan kungiyar ISWAP 40 a yankin Wulgo–Momaduru da ke karamar hukumar Ngala a jihar Borno
  • An gudanar da hare-haren ne da safiyar Talata, 10 ga watan Nuwamba, bayan jami'an tsaro sun gano tarin mayakan kungiyar a wani daji
  • Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren sun lalata babur tare da haddasa fashewar wasu abubuwa masu hadari a maboyar 'yan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Rahotanni sun bayyana cewa akalla mayakan kungiyar ISWAP 40 ne suka mutu sakamakon hare-haren sama.

An kai harin ne da jiragen yakin sojojin Najeriya suka kai a yankin Wulgo–Momaduru da ke karamar hukumar Ngala a jihar Borno.

An yi ruwan wuta kan yan ta'adda a Borno
Taswirar jihar Borno da ake fama da hare-haren Boko Haram. Hoto: Legit.
Source: Original

An gudanar da hare-haren ne karkashin rundunar Operation Hadin Kai, wadda ke jagorantar yaki da 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Zamfara: An sanar da sakamakon zaben fitar da gwanin dan majalisar tarayyar APC

Yadda sojoji suka gano maboyar mayakan ISWAP

A cewar Zagazola Makama, wata kafar yada labarai da ke mayar da hankali kan harkokin yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, an gudanar da aikin ne da sanyin safiyar Talata, 10 ga watan Nuwamba, bayan jami'an tsaro sun gano tarin mayakan ISWAP.

Majiyar ta bayyana cewa binciken sirri da sa ido daga sama sun gano mayakan ne a wani wuri da ke kimanin kilomita 1.5 daga arewa maso yammacin Wulgo–Momaduru.

Bayan samun wannan bayanin, sojoji suka kaddamar da hare-haren sama domin tarwatsa mayakan tare da kawar da barazanar da suke yi.

Zagazola Makama ya rawaito cewa majiyoyin tsaro sun ce harin farko da jiragen yakin suka kai ya hallaka mayakan ISWAP kusan 30 tare da lalata babur guda.

Haka kuma, an ga wasu fashe-fashe masu yawa a wurin bayan harin, lamarin da ke nuna yiwuwar lalata wasu abubuwa masu fashewa ko makamantansu.

Kara karanta wannan

An kama mutumin da ke sa mata a mota ya masu bidiyo tsirara

An sake kai hari kan mayakan da suka tsere

Rahoton ya kara da cewa yayin da aikin ke gudana, an ga wasu mayakan da suka tsira daga harin farko suna kokarin tserewa daga wurin.

Wasu daga cikinsu sun nemi mafaka a karkashin bishiyoyin da ke yankin domin kauce wa hare-haren jiragen yakin.

Sai dai jami'an sojoji sun ci gaba da sanya ido kan motsin mayakan, inda suka gano wani sabon taro na 'yan kungiyar ISWAP.

Bayan samun izinin kai sabon hari, jiragen yakin suka sake kai wani farmaki na musamman kan wurin da mayakan suka taru.

Binciken da aka gudanar bayan harin na biyu ya nuna cewa an kashe wasu mayakan 10, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu a hare-haren zuwa 40.

Muhimmancin hare-haren ga yaki da ISWAP

Zagazola Makama ya bayyana cewa hare-haren sun zama babban koma baya ga kungiyar ISWAP, musamman ganin yawan mayakan da suka taru a yankin.

Rahoton ya ce aikin ya kuma nuna muhimmancin tattara bayanan sirri, sa ido daga sama da kai hare-hare cikin kwarewa wajen tarwatsa taron 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Hatsabibin ɗan bindiga da ya addabi jama'a ya sheƙa barzahu a Katsina

Ya kara da cewa irin wadannan hare-hare na taimakawa wajen hana 'yan ta'adda sake shiri, karfafa maboyarsu ko kai hare-hare kan sansanonin sojoji da al'ummomin fararen hula.

Rahoton ya kuma bayyana cewa yankin Wulgo–Momaduru na da matukar muhimmanci wajen ayyukan tsaro a yankin tafkin Chadi, inda kungiyoyin 'yan ta'adda ke amfani da dazuzzuka da kauyuka masu nisa wajen gudanar da ayyukansu.

Sojoji sun kashe shugaban ISWAP

Mun ba ku labarin cewa sojojin Najeriya sun kashe Abu Hajara da Abul Walid, da wasu mayaƙan Larabawa biyu, yayin wani artabu da ISWAP a Kukawa.

Rundunar ta ce ta kwato makamai da alburusai da dama, tare da na’urorin sadarwa bayan fafatawar da ta gudana ranar 31 ga Oktoba, 2026.

Harin ya zo ne kwanaki uku bayan kashe ’yan ta’adda 55 a Buni Yadi, ciki har da wasu manyan kwamandojin ISWAP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.