Yan Bindiga Sun Shiga Gari Ido na Ganin Iso, Sun Yi Abin da Suke So kafin Isowar Jami'an Tsaro
- Mahara da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna, inda suka sace mutum 12
- Daga cikin waɗanda aka sace, mutum uku sun tsere sun koma gida, yayin da tara ke hannun masu garkuwa da su
- Dagacin ƙauyen ya ce idan aka haɗa waɗanda aka sace a hare-haren baya, jimillar mutanen ƙauyen da ke hannun ’yan bindiga a yanzu ta kai 14
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Wasu miyagun ’yan bindiga ne sun sace mutum 12 a ƙauyen Kurmin Wali da ke gundumar Afogo, ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Lamarin na baya-bayan nan ya faru ne a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, 2026, lokacin da maharan suka kai farmaki ƙauyen da misalin ƙarfe 9:14 na safe, inda suka yi awon gaba da mutane 12.

Source: Original
Mutum 4 sun gudo daga hannun maharan
Dagacin ƙauyen, Isiaku Danazumi, ya shaida wa jaridar Daily Trust a ranar Litinin cewa mutum uku daga cikin waɗanda aka sace sun samu damar tserewa sun koma gida, yayin da sauran tara ke hannun maharan.
Ya bayyana cewa idan aka haɗa mutanen tara da aka sace a harin ranar Lahadi da wasu mazauna ƙauyen biyar da aka sace a hare-hare biyu daban-daban a watan Oktoba, adadin mutanen da ke hannun ’yan bindigar ya kai 14.
“Eh, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 9:14 na safe. ’Yan bindiga sun sace mutane 12, amma uku sun dawo, yayin da sauran tara ke hannunsu.
“Amma a ranar 2 ga watan Oktoba, 2026, an kuma sace mutane biyu a lokacin damina. Haka kuma, a ranar 10 ga watan Oktoba, an sake sace wasu mutane uku. Don haka, jimillar mutanenmu 14 ne ke hannun ’yan bindigar a cikin daji,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta
An sanar da hukumomi a Kaduna
Basaraken ya ce sun sanar da hukumomin da abin ya shafa game da hare-haren, amma ya nuna damuwarsa kan yadda har yanzu ba a ɗauki wani kwakkwaran mataki na ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace ba.
Ya ƙara da cewa wasu jami’an tsaro sun isa ƙauyen a ranar Lahadi bayan maharan sun bar wurin, amma suka tafi ƙasa da awa guda da isarsu.
Ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ko ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan sabon harin ba.

Source: Facebook
An sace 'yan gudun hijira a Kaduna
Kun ji cewa yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan gudun hijira shida a Anguwan Baijuwa, Kaso, da ke ƙaramar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Mai kula da ’yan gudun hijira na Maraban Rido, Sule Adams, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sace mutanen ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026.
Asali: Legit.ng
