"Ana Kewar Buhari": Amaechi Ya Tuna Rayuwa a Lokacin Tsohon Shugaban Kasa

"Ana Kewar Buhari": Amaechi Ya Tuna Rayuwa a Lokacin Tsohon Shugaban Kasa

  • Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce ’yan Najeriya na kewar Buhari saboda yanayin rayuwa a lokacin mulkinsa
  • Amaechi ya yi iƙirarin cewa lokacin da gwamnatin Buhari ta bar mulki, dala ta kai kusan N600, yayin da litar fetur ba ta kai N300 ba
  • Ya zargi gwamnatin yanzu da almundahana, tare da ikirarin cewa an kama kusan dukkan ’yan kwangilar Ma’aikatar Sufuri domin binciken ayyukan da ya gudanar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufuri kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Rotimi Amaechi, ya ce ’yan Najeriya sun fara kewar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Amaechi ya bayyana cewa, a ra’ayinsa, rayuwa ta fi sauƙi a lokacin mulkin marigayi Buhari fiye da yadda take a ƙarƙashin gwamnatin APC mai ci yanzu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Matsayar kiristoci kan tikitin muslim muslim a Najeriya

Amaechi ya yi magana kan Buhari
Rotimi Amaechi da tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari, Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Channels Tv a shirin Sunrise Daily a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026.

Ya kwatanta zamanin Buhari da Tinubu

Amaechi ya ƙalubalanci ’yan Najeriya da su kwatanta yanayin rayuwarsu a lokacin mulkin Buhari da yadda suke rayuwa a yanzu.

Ya yi wannan batu ne yayin da yake bayyana dalilan da suka sa yake adawa da sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Tsohon ministan ya ambaci canjin kuɗin ƙasashen waje, farashin man fetur da zargin cin hanci da rashawa a matsayin wasu daga cikin abubuwan da ya kamata ’yan Najeriya su yi la’akari da su.

A cewarsa, Buhari ya taɓa cewa mutane za su yi kewarsa bayan ya bar mulki, kuma hakan ne yake ganin yanzu ya fara faruwa.

"A koyaushe ina son kawo maganar tsohon shugaban ƙasa, Buhari. Yakan ce, ‘Mutane za su nemi na dawo.’ Shin yanzu ’yan Najeriya ba suna cewa sun yi kewar tsohon Shugaba Buhari ba?

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fito da magana kan batun Tinubu bai da lafiyar tsayawa takara a 2027

“Dalilin da ya sa suke faɗin hakan shi ne, ku kwatanta rayuwarku lokacin da Shugaba Buhari yake raye kuma yake mulkin Najeriya da rayuwarku yanzu. Wanne za ku zaɓa?” In ji shi.

Amaechi ya kwatanta farashin dala da man fetur

Tsohon ministan ya yi iƙirarin cewa a lokacin da gwamnatin Buhari ta bar mulki, ana musayar dala kan kusan N600, yayin da farashin litar fetur bai kai N300 ba.

Ya kuma yi zargin cewa almundahana a gwamnatin yanzu ta fi abin da ake zargi ya faru a lokacin mulkin Buhari muni.

"Lokacin da muka bar mulki, dala tana kan N600, sannan litar fetur ba ta kai N300 ba. Idan ma an yi sata a gwamnatin Buhari, za a iya kwatanta ta da abin da ke faruwa yanzu?
"Abin da ke faruwa yanzu shi ne abin da nake kira ‘Ali Baba da ’yan fashi 40’.” In ji shi.
Amaechi ya ce ana kewar Buhari
Rotimi Amaechi na jawabi a wajen taro Hoto: Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi
Source: Facebook

Amaechi ya yi gargadi kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rotimi Amaechi, ya yi gargaɗin cewa hukuncin kotu kan shugabancin jam'iyyar na iya haddasa rikici idan ba a tafiyar da lamarin cikin hikima ba.

Amaechi ya bayyana cewa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke kan shugabancin jam'iyyar na iya haifar da mummunan sakamako ga ƙasar idan aka kasa shawo kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng