"Alaƙa Tsakanin Tinubu da Gwamna Ta Yi Tsami saboda Neman Takarar Shugaban Kasa a 2027"
- Gwamnan Oyo ya ce yana zargin burinsa na neman zama shugaban ƙasa a 2027 na iya haddasa rashin jituwa tsakaninsa da Tinubu
- Makinde ya tuna yadda ya goyi bayan Tinubu a zaɓen 2023 da kuma yadda ya taimaka wa Nyesom Wike a lokacin zaɓen fitar da gwani na PDP
- Ya ce Tinubu bai kira shi ba a lokacin da aka sace ɗalibai da malamai a ƙaramar hukumar Oriire
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce yana ganin burinsa na neman shugabancin Najeriya na iya zama sanadin rashin jituwa tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu, wanda ya mara wa baya a zaɓen 2023.
Gwamnan ya ce ba zai iya tabbatar da abin da ya haddasa sauyin dangantakar tasu ba, amma yana hasashen wasu mutane na iya gaya wa Tinubu cewa yana shirin tsayawa takara da shi a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Me ya lalata alakar Makinde da Tinubu?
Makinde ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise TV ranar Juma’a, inda yake magana kan yadda dangantakarsa da Tinubu ta sauya bayan ya taimaka wa shugaban ƙasar samun ƙuri’u a Jihar Oyo a zaɓen 2023.
Gwamnan ya ce:
“Gaskiya, hasashe kawai zan iya yi. Eh, don Allah, ka san mutane suna yawan magana, wataƙila wasu sun je sun gaya masa cewa, akwai yiwuwar Seyi ya tsaya takara da kai.’ Ban sani ba, wataƙila hakan ne ya haddasa rashin jituwa a tsakaninmu,” in ji shi.
Makinde ya kuma tuna ganawarsa da Tinubu a lokacin da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya gaya masa cewa zai kula da PDP a madadinsa gabanin zaɓen 2027.
Ya ce a lokacin ganawar, ya durƙusa kusa da Tinubu tare da bayyana masa cewa zai riƙe masa jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan
Gwamna ya jero dalilai 4 da suka sa zai yaƙi Tinubu a 2027 duk da ya goyi bayansa a 2023
Gwanna Makinde ya kare matsayinsa
Gwamnan ya ce ya goyi bayan Wike a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na PDP a 2023, lamarin da ya nuna cewa ba burinsa na neman takara ne ya sa ya ɗauki wannan mataki ba.
Ya kuma bayyana cewa wasu na kusa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, sun taɓa tuntuɓarsa domin ya tsaya takara tare da shi a zaɓen 2023, amma ya ƙi amincewa.
A cewarsa, a lokacin bai daɗe a matsayin gwamnan Oyo ko kuma a aikin gwamnati ba, don haka bai ga ya dace ya ɗauki irin wannan nauyi ba.

Source: Facebook
Makinde ya tuna abin da ya faru
Makinde ya kuma ce Tinubu bai kira shi ba a tsawon kwanaki 56 da ɗalibai da malamai da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire ta Jihar Oyo suka shafe a hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.
Ya ce ya yi ƙoƙarin ganawa da shugaban ƙasar ne saboda yana ganin ya kamata shugaban ya nuna damuwa idan wani yanki na Najeriya na fuskantar irin wannan matsala.
Gwamna Makinde ya zargi gwamnatin Tinubu
Kun ji cewa gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da amfani da Hukumar EFCC wajen tsoratar da gwamnonin adawa domin su koma APC.
Ya ce gwamnonin adawa da suka ƙi sauya sheƙa zuwa APC na iya fuskantar bincike da kuma yunƙurin shafa masu laifuffuka.
Asali: Legit.ng

