Malamin Musuluncin da Ya Yi Huduba Mafi Tasiri cikin Shekara 100 da Suka Gabata Ya Rasu

Malamin Musuluncin da Ya Yi Huduba Mafi Tasiri cikin Shekara 100 da Suka Gabata Ya Rasu

  • Duniyar musulunci ta yi rashi na daya daga cikin malaman da suka bayar da gudunmawa wajen sanar da mutane addini
  • Sheikh Al-Da'iyah Al-Muwaffaq Tayis Al-Jumaili wanda dan asalin kasar Kuwait ne ya koma ga Mahaliccinsa
  • Marigayin ya yi wata huduba wadda ake kyautatta zaton ita ce mafi tasiri a cikin shekara 100 da suka gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Doha, Qatar - Allah ya karɓi rayuwar ɗaya daga cikin manyan masu Da'awa a duniyar Musulunci, Sheikh Al-Da'iyah Al-Muwaffaq Tayis Al-Jumaili ɗan ƙasar Kuwait.

Sheikh Tayis, ga wanda bai san shi ba, shi ne asali da silar da kuma sirrin da ke bayan fitowar ɗaya daga cikin manyan masu Da'awar Musulunci a zamaninmu na yau, wato Dr. Abdurrahman Al-Sumait, Allah Ya jiƙan su baki ɗaya.

Al Jumaili ya rasu
Marigayi Sheikh Tayis Al-Jumaili Hoto: @NadeebQa
Source: Facebook

Shafin Doha News ya bayyana cewa an gudanar da jana'izar marigayin a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026 bayan sallar Magriba.

Kara karanta wannan

Jigo a ADC ya gano abin da Tinubu ke fargaba kan zaben 2027

Farfesa Mansur Sokoto a wani rubutu a shafinsa na Facebook ya ce akwai wata huɗubar da ya yi, wadda ga alama ita ce huɗubar da ta fi kowace tasiri a duniya cikin shekaru ɗari da suka gabata a wannan al'umma.

Labarin hudubar da marigayin ya yi

Sheikh Tayis Al-Jumaili ya yi huɗubar ne a wani Masallaci a Kuwait tun shekaru 40 da suka wuce, game da Sadaƙatul Jariya da falalar aikin alheri, da kuma yadda mutum zai bar tarihi mai kyau bayan mutuwarsa.

A cikin waɗanda suka halarci huɗubar akwai wata mata mai suna Hajiya Mawudhi Al-Sur. Bayan ta ji huɗubar, sai ta tafi ta sayar da wani filinta, ta kawo kuɗin ta ba Sheikh Tayis, ta ce ya kashe su a hanyar Allah da kuma taimakon Musulmi a duk inda ya ga ya dace.

Sheikh Tayis ya fara neman mutum amintacce da zai damƙa ma wannan kuɗin. Ya kafa kwamitin bincike wanda zai nemo yadda za a yi da kudin.

Kara karanta wannan

APC ta yi gyara a kwamitin kamfen din Tinubu bayan an yi abun kunya a idon duniya

Sai suka ji labarin wani likita matashi mai ƙwazon aikin addini da taimakon Musulmi, sunansa Abdurrahman Al-Sumait, matashi ne da ba kowa ya san shi ba a lokacin.

Sai suka kira shi suka ba shi kuɗin. Wannan matashin bai taɓa sanin Afirka ba sai a labarai kawai a wancan lokaci. Sai ya yi tafiya mai nisa da wannan kuɗin zuwa ƙasar Malawi, a can ne ya gina Masallaci da kuɗin.

Wannan Masallacin sai ya zama fitila mai haskaka Da'awa a Malawi, daga wannan aikin alherin ne aka samu Kwamitin Musulmin Malawi... sannan Kwamitin Musulmin Afirka... sannan daga baya ƙungiyar Agaji Kai Tsaye (Al-Awnul Mubashir) ta duniya.

Da Al-Sumait ya ga halin da Musulmi ke ciki a can Malawi, sai ya zauna kusan shekaru 30 yana Da'awa zuwa ga Musulunci har ya zama cikin mafi girman masu Da'awa a zamaninmu na yanzu.

Abin da ya faru sakamakon aikin da'awarsa

  • Mutane fiye da Miliyan 11 ne suka Musulunta a hannunsa.
  • Ya gina Masallatai fiye da 5,000.
  • Ya tona rijiyoyi fiye da 9,000.
  • Ya gina makarantu fiye da 800 da Jami'o'i 4.
  • Ya ɗauki nauyin marayu fiye da 15,000.

Kara karanta wannan

Mutanen Kano na cikin alheri, Gwamna Abba ya shirya rabon tallafin N50,000

Duk wannan, da izinin Allah, yana cikin mizanin lada na Sheikh Tayis Al-Jumaili wanda ya rasu da kuma a mizanin Hajiya Mawudhi Al-Sur. Allah Ya ji kan su baki ɗaya.

Wannan shi ne sakamakon huɗuba guda ɗaya wadda Allah ya sa mata albarka da tasiri, wacce ta kafa tarihi ln da da ba za a taɓa mantawa da shi ba a tarihin wannan al'umma.

Sheikh Tayis Al-Jumaili ya rasu
Malamin Musulunci, marigayi Sheikh Tayis Al-Jumaili Hoto: @NadeebQa
Source: Twitter

Kwamishina ya rasu a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Kwamishinan Kasuwanci na jihar, Tasiu Musa Shinkafi.

Marigayin Tasiu Musa Shinkafi ya rasu ne ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026 a Kaduna, yana da shekara 50, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng