Gwamnatin Najeriya Ta Gano Dokoki 268 da Suka Tsufa, Za a Soke Su
- Gwamnatin tarayya ta ce ta sake nazarin dokokin tarayya guda 932 da wasu ƙarin dokoki 731 domin sabunta kundin dokokin Najeriya
- Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa an gano dokoki 268 da suka tsufa, waɗanda ba za a saka cikin sabon kundin dokokin ba
- Ya ce an ware dokoki 664 domin saka su cikin sabon kundin dokokin Najeriya na shekarar 2025, wanda za a miƙa wa Shugaba Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta gano dokoki 268 da suka tsufa ko kuma aka soke a yayin aikin sake nazarin dokokin Najeriya.
Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja yayin gabatar da rahoton ƙarshe na kwamitin da aka kafa domin nazari kuma haɗa dokokin tarayya wuri guda.

Kara karanta wannan
Bayan faɗuwar ɗanyen mai a duniya, FCCPC ta waiwayo kan farashin fetur a Najeriya

Source: Twitter
Punch ta rahoto cewa Fagbemi ya ce kwamitin ya binciki dokokin tarayya guda 932 da wasu ƙarin dokoki 731, inda aka ware dokoki 664 domin saka su cikin sabon kundin dokokin Najeriya na 2025.
Dokokin da aka gano sun tsufa
Fagbemi ya bayyana cewa daga cikin dokoki 932 da kwamitin ya bincika, an gano 268 da suka tsufa, don haka ba za a saka su cikin sabon kundin ba.
Ya ce:
“An sanar da ni cewa kwamitin ya binciki dokokin tarayya guda 932 da wasu ƙarin dokoki 731. Daga cikin dokoki 932 da aka yi nazari a kansu, an gano 664 tare da ƙarin dokokin da suka shafe su domin saka su cikin kundin dokokin Najeriya na 2025, yayin da aka gano 268 da suka tsufa ko kuma aka soke.
“Waɗannan sakamakon na nuna babban ci gaba wajen samar da sabon kundin dokokin tarayya da aka sabunta kuma aka haɗa wuri guda.”
Ministan ya ce an gudanar da aikin ne domin sabunta tsarin dokokin Najeriya, musamman ganin cewa tun shekarar 2004 ba a sake yin cikakken haɗa dokokin ƙasar cikin kundin guda ba.
Ya ƙara da cewa sama da shekaru 20 sun wuce tun bayan wannan aikin, lokacin da ƙasar ta samu sauye-sauye da dama a fannonin dokoki, kundin tsarin mulki, cibiyoyi da fasaha.
Yadda aka sabunta dokokin
Fagbemi ya bayyana cewa ya kafa kwamitin ne a ranar 24 ga Oktoban 2024, tare da ba shi alhakin binciken dokokin tarayya da ƙarin dokokinsu.
Ya ce aikin kwamitin ya haɗa da gano dokokin da suka tsufa, gyara saɓani da maimaituwar wasu tanade-tanade, tare da samar da kundin dokoki mai sauƙin amfani da fahimta.

Source: Facebook
Ministan ya yaba wa kwamitin da Olawale Fapohunda (SAN) ya jagoranta, bisa aikin binciken shari'a, nazarin dokoki da haɗa bayanai da ya gudanar.
Ya ce kwamitin ya kafa ƙungiyoyin aiki guda 14 domin gudanar da aikin, tare da amfani da taruka da shawarwari na ƙwararru wajen tabbatar da ingancin sakamakon.
Hukumar DSS ta kama makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta cafke bindigogi kirar AK-47 guda 21 da manyan bindigogin PKT guda huɗu a wani yanki na jihar Sokoto.
Hukumar ta ce an kama makaman ne a Dawakawa da ke ƙaramar hukumar Goronyo, bayan sanya ido kan wasu mutanen da ake zargin masu safarar makamai ne.
Haka kuma, hukumar DSS ta kama mata da dama da ake zargin suna kai wa ’yan bindiga makamai a wasu jihohin Najeriya daban-daban.
Asali: Legit.ng

