Shugaban INEC ba Ya Son a Fitar da Takardun Tinubu, Ya Shigar da Bukata gaban Kotu

Shugaban INEC ba Ya Son a Fitar da Takardun Tinubu, Ya Shigar da Bukata gaban Kotu

  • INEC ta garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin neman soke umarnin da ya tilasta mata fitar da takardun takarar Bola Tinubu
  • Umarnin kotun ya fito ne a shari’ar da ake yi wa ɗan fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Omoyele Sowore, bisa zargin kiran Tinubu mai laifi
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce ba a miƙa masa sammacin da kansa ba, sannan takardun da ake nema ba a bayyana su daidai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe INEC, ƙarƙashin shugabanta, Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, ta shigar da ƙorafi a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan batun takardun Bola Tinubu.

INEC ta nemi soke sammacin da ya umarci hukumar ta fitar da takardun da suka shafi takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen gwamnan Jihar Legas na 1999 da kuma zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kotu ta nemi shugaban INEC ya gabatar da takardun takarar Tinubu

Amupitan.
Shugaban hukumar zaben Najeriya (INEC), Frafesa Joash Amupitan yayin ganawarsa da masu ruwa da tsaki Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Leadership ta ruwaito cewa takardun kotun da aka samu a ranar 10 ga Nuwamba, 2026, sun nuna cewa shugaban INEC, ta hannun lauyoyinsa, ya shigar da buƙatar neman soke umarnin da aka bayar a ranar 26 ga Oktoba, 2026.

Umarnin na da alaƙa da shari’ar da ake yi wa ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin bil’adama kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore.

Mai shari’a Mohammed Garba Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya bayar da umarnin a shari’a mai lamba FHC/CR/484/2025, tsakanin gwamnatin Najeriya da Sowore.

Takardun da kotu ta nema

Ana gurfanar da Sowore ne bisa wasu kalaman da ya yi inda ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin mai laifi.

Sammacin ya umarci shugaban INEC da ya gabatar da takardar Form CF001, ciki har da takardar rantsuwa da takardun shaidar karatu da Tinubu ya ce sun ɓace, waɗanda ya gabatar lokacin da yake neman takarar gwamnan Jihar Legas a 1999.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da ya soke takarar Atiku a zaɓen 2027

Haka kuma, kotun ta nemi Form CF001 na Tinubu da ya shafi takararsa ta shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ko kuma wata takarda makamanciyarta.

Dalilan INEC Na Ƙalubalantar matakin

A cikin buƙatar da ya shigar ta hannun lauyansa, Dakta Alex A. Izinyon, SAN, Amupitan na neman kotu ta ayyana sammacin a matsayin wanda ba shi da inganci, ba za a iya aiwatar da shi ba, kuma ya ƙunshi saɓani.

INEC ta yi zargin cewa ba a miƙa takardun umarnin kotun ga Farfesa Amupitan da kansa ba, kamar yadda doka ta tanada.

Lauyoyin INEC sun kuma yi iƙirarin cewa ko dai ba a bayyana takardun da ake nema daidai ba, ko kuma ba su wanzu a sigar da sammacin ya bayyana.

Bugu da ƙari, sun ce takardun ba su da alaƙa da shari’ar laifuffukan da ake yi wa Sowore.

INEC ba ta karbi takardun kotu ba

Kun ji cewa hukumar INEC ta ce har yanzu ba ta samu kwafin sahihin hukuncin kotu kan rikicin shugabancin ADC da takardun takarar Shugaba Bola Tinubu ba.

Shugaban hukumar, Joash Amupitan, ya ce ba sa daukar mataki bisa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta sai sun samu takardun doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262