Barayi Sun Shiga Masallaci Sun Sace Fankoki Sama da 20 a Kano
- Wasu da ake zargin barayi ne sun sace fanka 25 a masallacin Kanzul Mudalsam da ke unguwar Gwammaja a jihar Kano
- Mazauna yankin sun koka kan yadda satar kayayyaki, fadan daba da sauran laifuffuka ke ƙara zama barazana ga tsaron al’umma
- Wani jagoran al’umma ya ce mutane da dama na tsoron fita ko bin wasu hanyoyin yankin bayan ƙarfe 6:00 na yamma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Al’ummar unguwar Gwammaja da ke ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano sun nuna damuwa kan matsalar tsaro bayan wasu da ake zargin barayi ne sun sace fanka guda 25 daga saman masallacin Kanzul Mudalsam.
Satar ta faru ne a masallacin da ke kan titin hanyar Katsina a cikin birnin Kano, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin kan yadda miyagun laifuffuka ke ƙaruwa.

Source: Original
Freedom Radio ya wallafa a Facebook cewa jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Dala, Sagiru Nazifi Yakasai, ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar mai ɗauke da ranar 9 ga Nuwamba, 2026.
An koka kan satar kayan masallaci
A cikin sanarwar, Yakasai ya ruwaito bayanin Alhaji Salisu Sabon Titi, wanda hadimi ne kuma ɗan ƙungiyar Gwammaja Ina Mafita, kan matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Salisu ya bayyana cewa masu aikata laifin ba fankar masallaci kaɗai suke sata ba, har ma suna lalata turakun da aka ɗaura sola a kansu.
Ya ce irin waɗannan ayyuka na ƙara jefa al’umma cikin damuwa, musamman ganin yadda ake ci gaba da satar kayayyakin da aka tanada domin amfanin jama’a.
An sace babura 5, ana ƙwace wayoyi
Alhaji Salisu ya ƙara da cewa matsalar tsaro ta kai wani mataki da mutane da dama ba sa iya gudanar da harkokinsu cikin walwala.
Daily Trust ta wallafa cewa ya ce wasu mazauna yankin na tsoron bin hanyoyin Gwammaja bayan ƙarfe 6:00 na yamma saboda fargabar fuskantar barayi ko masu aikata laifuka.
Ya kuma yi zargin cewa a makon da ya gabata, an sace babura guda biyar tare da ƙwace wayoyin salula daga hannun wasu mutane.
Baya ga satar kayayyaki, ya ce fadan daba na daga cikin matsalolin da ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a yankin.

Source: Facebook
Alhaji Salisu ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da hukumar da ke yaƙi da shaye-shaye da fadan daba da su gaggauta ɗaukar matakan shawo kan matsalar.
Za a fara duba wata
A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci Musulmi a Najeriya su nemi ganin jinjirin watan Jimada Sani na shekarar 1448 bayan hijira a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba.
Sarkin Musulmin, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar NSCIA, ya buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan da idonsa ya sanar da sarakuna mafi kusa da shi domin isar da saƙon ga fadar mai alfarma.
Sanarwar da majalisar masarautar Sakoto ta fitar a ranar Lahadi, wadda Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa ranar Litinin ta yi daidai da 29 ga watan Jimada Ula.
Asali: Legit.ng

