Yadda Najeriya Ta Shiga Taitayinta bayan Matakin da Amurka Ta Ɗauka Kanta
- Jami’an Amurka sun ce Najeriya ta fara daukar matsalar rikicin addini da muhimmanci bayan Donald Trump ya sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da ke fuskantar barazana ta musamman
- Amurka ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kara tura jami’an tsaro, kare al’ummomin da ke cikin haɗari tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a hare-hare
- Wata masaniyar Amurka ta yi gargadin cewa bai kamata a dauki Kiristoci a matsayin wadanda suka fi kowa shan wahala daga matsalar tsaron Najeriya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jami’an gwamnatin Amurka sun bayyana cewa Najeriya ta fara daukar matsalar rikicin addini da muhimmanci bayan Shugaba Donald Trump ya sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da ke fuskantar barazana ta musamman (CPC).
Sai dai sun yi gargadin cewa akwai sauran ayyukan da ya kamata gwamnatin Najeriya ta gudanar domin kare al'ummomin da ke cikin haɗari da kuma hukunta wadanda ke da hannu wajen aikata laifuka.

Source: Facebook
Yadda Amurka ta zargi Najeriya
Jami'an sun bayyana hakan ne yayin wani zaman sauraron ra'ayi da Majalisar Dokokin Amurka ta gudanar kan matakan da Najeriya ke dauka domin dakile hare-hare kan al'ummomi bayan sanya ƙasar cikin jerin CPC, cewar Vanguard.
Shugaba Donald Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke da matukar damuwa kan 'yancin addini (CPC), bisa zargin tsananta wa Kiristoci da kisan kiyashi.
Tun daga lokacin, Najeriya da Amurka suka kulla yarjejeniyar hadin gwiwar soji domin yakar 'yan ta'adda a yankin Arewacin ƙasar, tare da kafa kwamitin hadin gwiwa da zai magance damuwar Washington kan rikicin addini.
Amurka ta bukaci Najeriya ta dauki matakai
Shugaban kwamitin kula da harkokin Afirka na majalisar wakilan Amurka, Chris Smith, ne ya shirya zaman domin duba matakan da Najeriya ke dauka kan hare-haren da ake kai wa al'ummomin da ke cikin haɗari.
Da yake jawabi, Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka, Frank Garcia, ya ce ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta kara tuntubar jami'an Najeriya domin dakile hare-hare kan Kiristoci da tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu a cikinsu.
Sai dai ya amince cewa har yanzu ana ci gaba da samun hare-haren, yana mai cewa Amurka na bukatar ganin sauye-sauye masu ma'ana a fannin tsaro.
Ya ce Washington na sa ran Najeriya za ta kara tura jami'an tsaro da 'yan sanda domin kare Kiristoci a yankin Middle Belt.
Haka kuma, ya ce akwai bukatar daukar matakan gaggawa bayan samun bayanan sirri kan hare-haren da ake shirin kai wa, tare da karfafa tsarin shari'a domin hukunta masu laifi.
Garcia ya ce:
"Abin da muke bukata shi ne ganin sakamako, wato kare al'ummomin Kiristoci a yankin Middle Belt ta hanyar kara tura jami'an tsaro da jami'an tabbatar da doka, daukar matakan gaggawa bayan samun gargadin hare-hare, hukunta masu laifi da karfafa hadin gwiwar sojojin ƙasashen biyu."
Amurka ta bukaci a soke dokokin batanci
Shi ma Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da dimokuradiyya, 'yancin dan Adam da kwadago, Riley Barnes, ya ce Amurka na ci gaba da bukatar gwamnatin Najeriya ta soke dokokin da suka shafi batanci ga addini.
Ya ce idan ba za a iya soke dokokin ba, to a kalla ya kamata gwamnati ta dakatar da amfani da su wajen gurfanar da mutane, cewar Punch.
Barnes ya bayyana cewa matakin Trump na sake sanya Najeriya cikin jerin CPC ya sa gwamnatin ƙasar ta fara daukar matsalar rikicin addini da sauran abubuwan da suka shafi hakan da muhimmanci.
Amurka za ta sa ido kan zaben Najeriya
A wani labarin, an ji cewa yan majalisar dokokin Amurka sun ce za su sa ido sosai kan zaɓen shugaban ƙasar Najeriya na watan Janairun 2027.
Dan majalisa Riley Moore ya ce dole ne Amurka ta tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun samu damar zaɓen shugabanninsu cikin ’yanci.
Frank Garcia ya ce har yanzu ba a samu isasshen ci gaba wajen magance matsalolin tsaron Najeriya ba, duk da haɗin gwiwar ƙasashen biyu.
Asali: Legit.ng


