Akwai Matsala: Obi da Magoya Bayansa Sun Zubar wa Najeriya Kima a Idon Duniya
- Peter Obi da magoya bayan jam’iyyar NDC sun ƙi rera sabuwar taken Najeriya yayin wani taron ganawa da jama’a da suka gudanar a Legas
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya haɗu da Funso Doherty da sauran magoya bayansa wajen rera tsohuwar taken ƙasar mai suna ‘Nigeria, We Hail Thee’
- Matakin nasu ya zo ne bayan wasu ’yan daba sun kai hari wurin taron da makamai, lamarin da ya tilasta wa mahalarta taron neman mafaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC, da magoya bayansa sun yi fatali da sabuwar taken Najeriya.
Magoya bayan Obi sun ƙi amincewa da sabuwar taken Najeriya, inda suka rera tsohuwar taken ƙasar a wani taron jama’a da aka gudanar a Legas.

Source: Facebook
Obi, masoyansa sun ki rera taken Najeriya
Jaridar TheCable ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamba, 2026, yayin taron tattaunawa da jama’a da Obi da magoya bayan jam’iyyar suka halarta.
A wani bidiyo da Channels TV ta hada a YouTube, an ga Obi tare da Funso Doherty, ɗan takarar gwamnan Legas na jam’iyyar NDC, da sauran magoya bayan jam’iyyar sun ƙi tashi tsaye domin rera sabuwar taken ƙasar.
Hakan ya sa mai gabatar da taron ya sauya zuwa tsohuwar taken Najeriya, wadda mahalarta taron suka rera cikin nishaɗi.
Obi ya kuma nuna goyon bayansa ga matakin ta hanyar fuskantar taron yayin da suke rera taken, tare da ɗaga yatsu biyu a hannayensa, abin da ke wakiltar tambarin jam’iyyar NDC.
An kai hari wurin taron
Wannan lamari ya faru ne bayan da wasu ’yan daba suka kutsa kai wurin taron ɗauke da adduna, sanduna da duwatsu, lamarin da ya haddasa rudani tare da tilasta wa mahalarta taron tserewa domin tsira.
A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi ya samu ƙuri’u 582,354 a Legas, jihar da jam’iyyar APC ke da babban rinjaye. A lokacin, Obi ya tsaya takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party (LP).
Tarihin sauya taken Najeriya
A ranar 29 ga watan Mayun 2024, Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar da ta dawo da tsohon taken Najeriya mai suna ‘Nigeria, We Hail Thee’.
An fara amfani da taken ne a shekarar 1960, lokacin samun ’yancin kai, kafin aka maye gurbinta da ‘Arise, O Compatriots’ a shekarar 1978.
Taken Najeriya da aka dawo amfani da shi a yanzu yana ba wasu yan Najeriya wahalar rike wa fiye da wanda aka maye gurbinsa da shi.
Alkawarin da Obi ya yi ga ƴan Najeriya
Mun kawo muku cewa dan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya ce gwamnatinsa za ta magance matsalar raba mutane da muhallansu saboda rikice-rikici.
Obi ya yi alkawarin haɗa kan ’yan Najeriya da tabbatar da tsaron rayukansu, musamman a jihohin Plateau da Benue.
Ya ce zai ɗauki gwamnatinsa a matsayin wadda ta gaza idan wani ɗan Najeriya yana sansanin ’yan gudun hijira bayan watanni 18.
Asali: Legit.ng

