Iyalan Tinubu na Ta Samun Sarauta, Sarakunan Zamfara Sun Yi Wa Remi Nadi

Iyalan Tinubu na Ta Samun Sarauta, Sarakunan Zamfara Sun Yi Wa Remi Nadi

  • Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta samu sarauta daga Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar Zamfara
  • An naɗa ta sarautar ne ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, yayin ziyararta Zamfara domin halartar taron mata na APC a Gusau
  • Naɗin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa, ya samu sarautar Dan Zaki Gwandu a Jihar Kebbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Zamfara ta naɗa uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, sarautar gargajiya ta “Jagaban Matan Zamfara.”

An naɗa ta wannan sarauta ne ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, yayin ziyarar da ta kai jihar domin halartar babban taron mata na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shirin ƙarfafa musu gwiwa a Gusau.

An ba Remi Tinubu sarauta a Zamfara
Remi Tinubu lokacin da aka yi mata a Zamfara Hoto: @KukoyiBusola
Source: Facebook

Busola Kukoyi, mataimakiya ta musamman ga uwargidan shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, ce ta sanar da naɗin a cikin wata sanarwa da ta wallafa ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamban 2026 a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Tsaro ko tazarcen Tinubu: Matawalle ya bayyana babban burinsa a 2027

Yadda aka sanar da naɗin sarautar

Sanarwar ta bayyana cewa Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Zamfara ce ta ba Oluremi Tinubu sarautar yayin ziyarar da ta kai musu a gefen taron mata na APC.

A cewar sanarwar, majalisar sarakunan gargajiyar sun ba da sarautar ne ga uwargidan shugaban kasar a ranar Juma'a, 13 ga watan Nuwamban 2026.

Sai dai sanarwar ba ta yi ƙarin bayani kan dalilan da suka sa majalisar ta zaɓi ba ta wannan sarauta ba.

Taron mata na APC a Zamfara

Taron da aka gudanar a Gusau na daga cikin shirye-shiryen da APC ke yi domin ƙara wayar da kan mata da jawo hankalinsu gabanin babban zaɓen 2027.

Jam’iyyar na ƙoƙarin ƙarfafa goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu domin neman sake zaɓensa a karo na biyu.

Ziyarar uwargidan shugaban ƙasar ta kuma biyo bayan wasu shirye-shiryen wayar da kan mata da APC ke gudanarwa a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027

A farkon makon, sashen yaɗa manufofin jam’iyyar kan wayar da kan mata ya kai ziyara kasuwanni, asibitoci da wasu al'ummomi a Jihar Jigawa domin ƙarfafa hulɗa da jama'a a matakin ƙasa.

Sarautar gargajiya ga manyan baƙi

A al’adar Najeriya, sarakunan gargajiya kan naɗa shugabannin siyasa da sauran manyan mutane sarautu a matsayin alamar girmamawa da karramawa.

Naɗin Oluremi Tinubu ya zo ne kwanaki kaɗan bayan an naɗa Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Tinubu, sarautar Dan Zaki Gwandu.

Mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ne ya naɗa Seyi Tinubu sarautar a Jihar Kebbi.

Remi Tinubu ta samu sarauta a Zamfara
Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu Hoto: @KukoyiBusola
Source: Twitter

Alkawarin Remi kan tazarcen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta yi alkawari kan tazarcen mijinta, mai girma Shugaba Bola Tinubu.

Remi Tinubu ta ce za ta sanya zannuwan Akwete idan mijinta, Shugaba Bola Tinubu, ya samu wa’adi na biyu a matsayin shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng