Yadda Wata Mata Ta Sace 'Yar Dan'uwanta har Ta Nemi Kudin Fansa N10m
- ’Yan sanda sun kama wata mata a ranar 10 ga Nuwamba, 2026, a gundumar Bela da ke ƙaramar hukumar Bungudu
- Ana zargin ta da sace ƙaramar yarinya mai shekara uku tare da neman Naira miliyan 10 kafin a sake ta
- An ceto yarinyar bayan shafe kusan makonni biyu a hannun waɗanda suka yi garkuwa da ita, sannan aka haɗa ta da iyayenta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta kama wata mata mai shekara 26 bisa zargin sace ƙaramar ’yar yayanta mai shekara uku, tare da neman kuɗin fansa har Naira miliyan 10.
An ce yarinyar ta shafe kusan makonni biyu a hannun wadda ake zargi kafin jami’an ’yan sanda su yi nasarar kuɓutar da ita.

Source: Original
Yadda aka sace yarinyar
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamban 2026 wadsa Legit Hausa ta samu.
An kama wadda ake zargin ne a ranar 10 ga Nuwamba, 2026, a gundumar Bela da ke ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
A cewar sanarwar, mahaifin yarinyar, Abdulganiyu Sahabi, mazaunin ƙaramar hukumar Kaura Namoda, ya kai rahoton sace ’yarsa ga jami’an sashen binciken sirri na rundunar a ranar 30 ga Oktoban 2026.
Mahaifin ya shaida wa ’yan sanda cewa wani mutum da ba a san ko wanene ba ne ya yi garkuwa da ’yarsa a ranar 28 ga Oktoba.
Ya ƙara da cewa washegari, ya samu kiran waya daga wata ɓoyayyar lamba, inda mai kiran ya ce yana riƙe da yarinyar tare da neman Naira miliyan 10 domin sakin ta.
Yadda ’yan sanda suka ceto yarinyar
Sanarwar ta ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Ahmad Bello, ya umarci sashen binciken sirri da ya gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da kuɓutar da yarinyar cikin aminci.
Ta ƙara da cewa tattara bayanan sirri, binciken fasaha da haɗin gwiwa da wasu abokan hulɗa sun taimaka wajen gano tare da kama wadda ake zargin, da kuma ceto yarinyar.
Binciken farko ya nuna cewa matar da aka kama ƙanwar mahaifin yarinyar ce. An ce suna da uba ɗaya, amma uwa kowa da ta sa.
Rundunar ta bayyana cewa wadda ake zargin ta amsa hannu a laifin lokacin da jami’an tsaro suka yi mata tambayoyi.
An mayar da yarinyar ga iyayenta
’Yan sandan sun ce har yanzu suna ci gaba da bincike domin gano cikakken yadda lamarin ya faru, da kuma gano ko akwai wasu mutanen da suka taimaka wajen aikata laifin.
Bayan ceto ta, an kai yarinyar domin duba lafiyarta. Daga bisani, aka mayar da ita hannun iyayenta a ranar 12 ga Nuwamba, 2026, bayan kammala binciken lafiyarta.
Kwamishinan ’yan sandan ya yaba wa jami’an sashen binciken sirri bisa ƙwarewa da jajircewar da suka nuna, waɗanda suka taimaka wajen ceto yarinyar.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun sace mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani magidanci da wasu mutum biyar da ke tafiya da gawar matarsa daga Jihar Kano zuwa garinsu a jihar Benue.
Maharan sun sace mutanen ne a daren ranar Juma’a a yankin Adoka da ke ƙaramar hukumar Otukpo, yayin da suka bar gawar matar a cikin motar da suke ciki.
Asali: Legit.ng

