Da Gaske Gwamnatin Tarayya Ta Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta da Boko Haram?

Da Gaske Gwamnatin Tarayya Ta Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta da Boko Haram?

  • Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa ta yi magana kan batun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da Boko Haram, ISWAP ko wasu ƙungiyoyin masu aikata laifufffuka
  • Manjo Janar Samaila Uba ya ce sojoji na ci gaba da matsin lamba kan ’yan ta’adda, tare da kashe wasu, kama waɗanda ake zargi da ceto mutanen da aka sace
  • Rundunar ta ce ayyukanta ba su takaita ga Boko Haram da ISWAP ba, domin sun haɗa da masu garkuwa da mutane da sauran ’yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa ta musanta cewa Gwamnatin Tarayya ta kulla wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙungiyar Boko Haram, ISWAP ko wasu ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Rundunar sojojin ya bayyana cewa za a ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

An musanta kulla yarjejeniya da Boko Haram
Hafsan hafsoshi, Janar Olufemi Oluyede da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Dauda Lawal, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedkwatar Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.

Batun kulla yarjejeniya da Boko Haram

Wannan musun ya biyo bayan wani rahoto da ya yi ikirarin cewa Gwamnatin Tarayya ta shiga yarjejeniyar sirri da ɓangaren Boko Haram da Bakura Doro ke jagoranta.

Rahoton ya ce yarjejeniyar ta taimaka wajen samun ɗan sauƙin matsalar tsaro a wasu sassan Arewa maso Gabas na tsawon kusan watanni uku.

Rahoton, wanda ya dogara da bayanan wasu mutane uku da ke da alaƙa da manyan mambobin Boko Haram, ya yi ikirarin cewa yarjejeniyar ta fara aiki ne tun watan Yuni, kuma ana sa ran tsawaita ta.

Rundunar ta ce babu yarjejeniyar tsagaita wuta

Sai dai da yake magana a taron, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla da Boko Haram.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya ji dadin giyar mulki, ya cika baki kan girman jam'iyyar a Najeriya

Ya bayyana cewa sojoji na ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai lamba, tare da samun nasarori a hare-haren da suke kaiwa.

Samaila Uba ya ce yawan ’yan ta’addan da aka kashe, waɗanda ake zargi da aka kama da kuma mutanen da aka ceto daga hannun masu garkuwa da su, na nuna cewa sojoji ba su sassauta ayyukansu ba.

“Dangane da batun ko akwai yarjejeniyar tsagaita wuta da Boko Haram, ina so in bayyana a sarari cewa babu wani abu makamancin haka.

“Idan aka yi la’akari da ’yan ta’addan da aka kashe, waɗanda ake zargi da aka kama, mutanen da aka ceto da sauran nasarorin da aka samu a ayyukanmu, a bayyane yake cewa ba mu sassauta ba.
“Za mu ci gaba da matsa wa waɗannan miyagun ƙungiyoyi lamba.”

Sojoji ba su tsaya kan Boko Haram kadai ba

Daraktan ya ƙara da cewa ayyukan rundunar sojoji ba su takaita ga yaƙi da Boko Haram ko ISWAP kaɗai ba.

Ya ce ana kuma kai hare-hare kan masu garkuwa da mutane da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai waɗanda ke barazana ga rayuka da tsaron ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Nasara babba: Sojoji sun kashe shugabannin ISWAP da mayaka Larabawa a Borno

A cewarsa, duk wani rukuni da ya ɗauki makami domin cutar da fararen hula na cikin waɗanda rundunar ke kai wa samame.

“Ayyukanmu ba su takaita ga Boko Haram ko ISWAP ba. Suna kuma shafar masu garkuwa da mutane da sauran miyagun ƙungiyoyi waɗanda ke ɗaukar makami domin kai hari kan ’yan ƙasa marasa laifi.” In ji shi.

Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a faɗin ƙasar domin murƙushe ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kare rayukan al’umma.

DHQ ta musanta tsagaita wuta da Boko Haram
Kakakin hedkwatar tsaro ta kasa, Samaila Uba Hoto: Defence Headquarters
Source: Facebook

Sojoji sun kashe shugabannin ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun Operation Hadin Kai sun kashe manyan shugabannin ƙungiyar ISWAP guda huɗu, ciki har da Larabawa biyu a jihar Borno.

Sojojin sun kuma kashe wani babban kwamanda, tare da wasu mayakan ƙungiyar a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng