Shugaban EFCC Ya Ga Abin Mamaki a kan Gwamnan Zamfara
- Shugaban hukumar EFCC, Olanipekun Olukoyede, ya bayyana jihar Zamfara a matsayin misali na sauyin shugabanci a ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal
- Olukoyede ya ce sababbin filayen jiragen sama, titunan da ka shimfida da kwalta da fitilun hasken rana a Gusau na daga cikin alamomin ci gaban jihar
- Shugaban hukumar ya kuma yaba wa gwamnatin jihar kan inganta sakamakon ɗalibai a jarabawar NECO da WAEC cikin shekaru uku da suka gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gusau – Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Olanipekun Olukoyede, ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal kan sauye-sauyen da ya ce ya gani a jihar Zamfara.
Olukoyede ya bayyana hakan ne yayin gabatar da babban jawabi a bikin cika shekaru 30 da kafuwar jihar Zamfara, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan ya wallafa a Facebook cewa Olukoyede ya bayyana cewa ya gudanar da bincike kan jihar da gwamnan kafin ya amince da gayyatar halartar taron.
Shugaban EFCC ya halarci taron
Daily Trust ta wallafa cewa Olukoyede ya ce bisa ƙa'idojin aiki da ɗabi'ar da ofishinsa ke buƙata, ba ya halartar tarukan siyasa ko zuwa gidan gwamnati.
Sai dai ya bayyana cewa gayyatar da aka yi masa ta sa ya gudanar da bincike domin fahimtar abin da ke faruwa a Zamfara, inda ya ce abubuwan da ya gani suka gamsar da shi.
Ya ce:
“Saboda ƙa'idojin da aikina ke buƙata, ba na halartar tarukan siyasa, kuma ba na zuwa gidan gwamnati bisa ƙa'ida. Amma da na samu wannan gayyata, wani abu ya gaya mini in amince domin in ga abin da ke faruwa a can.”
Ya ƙara da cewa bayan nazarin sauye-sauyen da ya ce ya gani a jihar cikin shekaru uku, sai ya nemi izinin Shugaba Bola Tinubu domin halartar bikin.
Abubuwan cigaba a Zamfara
Shugaban EFCC ya lissafa sabon filin jirgin sama, titunan da aka shimfiɗa da kwalta da kuma sanya fitilu masu aiki da hasken rana a Gusau a matsayin wasu daga cikin alamomin ci gaban da aka samu.
Haka kuma, ya yaba wa gwamnatin Lawal kan ingantuwar sakamakon ɗaliban jihar a jarabawar kammala sakandare ta NECO da WAEC.
A cewarsa, waɗannan matakai sun nuna cewa gwamnatin jihar na aiwatar da sauye-sauye bisa tsari, kuma sun dace da taken lacca ta cika shekaru 30.

Source: Facebook
Olukoyede ya ce gayyatar shugaban EFCC zuwa gidan gwamnati domin yin jawabi ga al'ummar jihar, duk da ƙa'idojin da ke tattare da ofishinsa, na buƙatar gwamna mai gaskiya da jajircewa wajen dimokuraɗiyya.
An nada sarakuna a Zamfara
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Dauda Lawal ya miƙa sandar mulki ga Sarkin Gusau na 16, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello II, tare da wasu sarakuna 18 a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC
Gwamnan ya buƙaci sarakunan gargajiya da su haɗa kai da gwamnatinsa wajen dawo da zaman lafiya da samar da tsaro mai ɗorewa a jihar.
A nasa ɓangaren, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello II ya yi alƙawarin kafa shugabanci nagari, inganta tsaro da ƙarfafa haɗin kan al'umma.
Asali: Legit.ng

