Sarkin Musulmi Ya ba Sheikh Bala Lau Lambar Yabo Ta Musamman

Sarkin Musulmi Ya ba Sheikh Bala Lau Lambar Yabo Ta Musamman

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya karrama shugaban Izala na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau
  • An bai wa malamin lambar yabon mai suna “Sheikh Abdullahi Fodiyo Exemplary Prize for Knowledge and Scholarship” ta shekarar 1448AH/2026
  • An karrama Sheikh Bala Lau ne bisa gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimin Musulunci da yaɗa koyarwar Sunnah ta Annabi Muhammad (SAW)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya karrama shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, da lambar yabo ta musamman.

An bai wa malamin lambar yabon ne a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2026, bisa gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimi, hidimtawa addinin Musulunci da yaɗa koyarwar Sunnah.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe babban dan agajin Izala, Bala Lau ya yi magana

Sarkin Musulmi Sheikh Abdullahi Bal Lau
Lokacin da Sultan zai karrama Sheikh Bala Lau. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Ƙungiyar Izala ta sanar da karramawar ne a shafinta na Facebook, inda ta bayyana jin daɗinta kan wannan nasara da shugabanta ya samu.

Dalilin karrama Bala Lau

Lambar yabon da aka bai wa Sheikh Bala Lau ita ce “Sheikh Abdullahi Fodiyo Exemplary Prize for Knowledge and Scholarship” ta shekarar 1448AH/2026.

A cikin wasiƙar sanar da karramawar, Sarkin Musulmi ya bayyana cewa an yanke shawarar karrama malamin ne bayan nazari da shawarwari kan irin gudunmawar da ya bayar a fannonin ilimi da addini.

Ya ce sadaukarwar Sheikh Bala Lau wajen yaɗa ilimi da kyawawan koyarwar Musulunci ta sa ya cancanci samun wannan girmamawa.

Addu'ar da Sultan ga Ba Lau

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi addu'ar Allah Ya karɓi ayyukan malamin a matsayin ibada, Ya ƙara masa lafiya da tsawon rai.

Haka kuma, ya roƙi Allah Ya sanya Sheikh Bala Lau ya ci gaba da zama fitila mai haskaka al'ummar Musulmi, musamman wajen kiyaye kyawawan manufofin Daular Sakkwato.

Kara karanta wannan

Tinubu ya zabi manyan hadiminsa da gwamnoni 5, ya shirya masu liyafa a Makkah

Izala ta ce wannan karramawa na nuna irin muhimmancin da ake bai wa hidimar ilimi da addini, tare da ƙarfafa gwiwar malamai da masu yaɗa koyarwar Musulunci.

Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban Izala na kasa, Sheikh Bala Lau. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Babban sakataren JIBWIS na ƙasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, tare da Alaramma Nasiru Salihu Gwandu, na cikin waɗanda suka raka shugaban ƙungiyar zuwa wajen taron karramawar.

Ƙungiyar ta taya shugaban nata murnar samun wannan lambar yabo, tare da addu'ar Allah Ya sanya ta zama alheri, Ya ƙara masa ikhlasi da dacewa.

An kashe dan agajin Izala

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa wani mamba na ƙungiyar JIBWIS, Abubakar Yusuf Sokoto, na cikin jami'an tsaro biyar da suka rasa rayukansu a harin 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Marigayin, wanda ɗan sanda ne, ya rasu ne ranar Lahadi lokacin da wasu 'yan bindiga suka yi wa tawagar jami'an tsaro kwanton ɓauna a jihar.

Shugaban JIBWIS na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan marigayin da sauran mambobin ƙungiyar bisa wannan babban rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng