An Rasa Rayuka da Dama da Yan Bindiga Suka Far Wa Mutane da Yammacin Ranar Juma'a
- Yan bindiga da ake zargin Fulani Makiyaya ne sun kai sababbin hare-hare kan wasu al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Ukum ta Jihar Benue
- Wani mazaunin yankin ya ce an kashe mutum tara, amma an gano gawarwaki shida kacal a lokacin haɗa wannan rahoton
- Wata majiya mai tushe a ɓangaren tsaro ta ce har yanzu ba a ga wasu mazauna yankin ba bayan hare-haren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue, Nigeria - Wasu miyagun yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya masu dauke da makamai ne sun sake kaddamar da hare-hare kan jama'a a jihar Benue.
An ruwaito cewa an kashe aƙalla mazauna yankin shida a sababbin hare-haren da aka kai garuruwan Tse-Nyaku, Biliji da wasu kaiyuka a Mbatian da Mbazum, Ƙaramar Hukumar Ukum ta Jihar Benue.

Source: Original
An kai sababbin hare-hare a Benue
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hare-haren sun faru ne a yammacin ranar Juma’a, a cewar wani mazaunin Mbatian mai suna Aondofa David.
Wata majiya mai tushe a ɓangaren tsaro ta kuma shaida wa manema labarai yayin da aka tuntube ta cewa an nemi wasu wasu mazauna yankin an rasa bayan hare-haren.
Wani mazaunin kauyen Biliji, ɗaya daga cikin al’ummomin da abin ya shafa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da kai wadannan hare-hare.
Yan bindiga sun kashe mutum 9
Mutumin ya ce sun ji labarin cewa an kashe mutane tara, sai dai an gano gawarwaki shida ne kacal a har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
“Maharan, waɗanda ake zargin Fulani makiyaya ne masu ɗauke da makamai, a farko sun kai hare-hare wasu ƙauyuka a Mbazum Mbaterem kafin daga bisani su wuce zuwa kauyukan da ke yankin Mbatian.
"An kashe mutane tara, amma kawo yanzu an gano gawarwaki shida kacal,” in ji mazaunin.
Da aka kira shugaban Ƙaramar Hukumar Ukum, Jonathan Modi, ta waya domin jin ta bakinsa, bai amsa kiran ba.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take
Sai dai ɗaya daga cikin mataimakansa ya ce shugaban yana cikin aikin taimaka wa waɗanda lamarin ya shafa ne shi yasa bai samu damar ɗaga waya ba.

Source: Twitter
Abin da yan sanda suka ce
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue, DSP Peter Orchia Aondongu, ya ce har yanzu bai samu rahoton hare-haren daga jami’an tsaro da ke yankin ba.
“Har yanzu ban samu rahoto a hukumance jan harin da kake magana a kai ba. Idan na samu cikakkun bayanai, zan dawo gare ka,” in ji shi.
Yan bindiga sun kashe mutane 3
Kun ji cewa an kashe aƙalla mutane uku, ciki har da yaro mai shekaru uku, a wani hari da ake zargin makiyaya masu ɗauke da makamai sun kai a jihar Benue.
Rahotannin da aka samu sun bayyana cewa maharan sun shiga cikin garin ne a yammacin ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2027, inda suka jikkata wasu mazauna yankin da dama.
Asali: Legit.ng
