An Fara Gargadi kan Sauya Lokacin Zaben 2027 saboda Cutar Ebola

An Fara Gargadi kan Sauya Lokacin Zaben 2027 saboda Cutar Ebola

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi gargaɗin cewa bai kamata a soke gangamin siyasa ko a sauya lokacin babban zaɓen 2027 saboda Ebola
  • Adebayo ya ce samun mutum guda da aka tabbatar ya kamu da cutar bai isa a ayyana barkewar annoba ba, yana mai cewa za a iya kare lafiyar jama'a ba tare da kawo cikas ga tsarin zaɓe ba
  • Ya bayyana hakan ne yayin wani liyafar cin abinci da shugabannin kwamitin kamfen dinsa suka shirya, inda ya sanar da cewa an fassara manufofinsa zuwa harsunan Najeriya daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na soke gangamin siyasa ko sauya lokacin zaɓen 2027 saboda barkewar cutar Ebola.

Kara karanta wannan

Wike ya faɗi abin da zai hana Obi zama shugaban ƙasa, ya tuna mummunan halinsa 1

Adebayo ya bayyana cewa samun mutum guda da aka tabbatar ya kamu da cutar bai isa a ayyana barkewar annoba ba, yana mai jaddada cewa Najeriya za ta iya kare lafiyar jama'a ba tare da dakatar da harkokin siyasa da zaɓe ba.

Adewole Adebayo na SDP
Dan takarar shugaban kasa na SDP, Adewole Adebayo. Hoto: Adewole Adebayo
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ɗan takarar ya bayyana hakan ne a yayin wani liyafar cin abinci da shugabannin kwamitin yaƙin neman zaɓensa suka shirya a Abuja ranar Lahadi.

Adebayo ya yi gargadi kan Ebola

Adebayo ya ce Najeriya ta taɓa shawo kan barkewar cutar Ebola a shekarar 2014, a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, inda ya ce an gudanar da ayyukan yaƙi da cutar cikin gaskiya da bayyana bayanai ga jama'a.

Ya zargi gwamnatin jam'iyyar APC da rashin bayyana cikakkun bayanai kan wasu lamura, yana mai cewa hakan na haifar da shakku game da yadda ake tafiyar da matsalar cutar a yanzu.

A cewarsa, bai kamata a soke gangamin siyasa, tarukan yaƙin neman zaɓe ko kuma a sauya babban zaɓen 2027 saboda samun mutum guda da ya kamu da cutar ba.

Ya ce:

“Ebola ba ita ce babbar matsalar lafiya da muke da ita a Najeriya ba. Matsalar ita ce duk abin da gwamnatin APC ta tattauna ko ta jagoranta, akwai yaudara da ɓoye gaskiya a ciki.

Kara karanta wannan

Yadda 'yunwa' za ta ruguza lissafin Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027

“Mutum guda da aka tabbatar ya kamu da Ebola bai isa a ce an samu barkewar annoba ba. Mun taɓa fuskantar cutar a Najeriya a lokacin Goodluck Jonathan, lokacin da Dakta Onyebuchi Chukwu yake Ministan Lafiya."

Bayanin da gwamnati ta yi

Gargaɗin na Adebayo ya zo ne bayan Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a, Farfesa Muhammad Pate, ya bayyana cewa babu buƙatar gaggawa ta soke gangamin siyasa, taruka ko wasu manyan tarurruka saboda cutar Ebola.

Sai dai ministan ya ce gwamnati za ta yi la'akari da sanya takunkumi idan yanayin cutar ya tsananta.

Da yake magana yayin taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis da ta gabata, Pate ya ce duk wani mataki na hana taruka zai dogara ne kan shaidar kimiyya da shawarwarin ƙwararrun masana kiwon lafiyar jama'a.

Taswirar FCT, Abuja
Taswirar FCT, Abuja. Hoto: Legit
Source: Original

Nafiu Bala ya kafa kwamitin kamfen

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani ɓangare na jam'iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe ya sanar da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa na babban zaɓen 2027.

Ɓangaren ya kuma bayyana Farfesa Chris Uba a matsayin ɗan takararsa na shugaban ƙasa, yayin da aka zaɓi Dakta Shamsudeen Barkindo a matsayin abokin takararsa.

Sanarwar ta bayyana Nafiu Bala Gombe, wanda ke jagorantar tsagin, a matsayin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, yayin da aka naɗa Farfesa Ahmed Jidda Balarabe a matsayin darakta-janar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng