Masu Shirin Magudi a Zaben 2027 na Ruwa, an kai lamarin gaban Shugaba Trump
- Mike Igini ya rubuta wasiƙa ga Donald Trump yana neman Amurka ta danganta hulɗarta da Najeriya da sahihancin zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Ya gabatar da wani tsari wanda ya ƙunshi sa ido kan zaɓe da kakaba takunkumi ga waɗanda aka tabbatar sun aikata maguɗi
- Igini ya nemi a hukunta jami’an INEC, wasu ma’aikatan shari’a da jami’an tsaro da aka samu da hannu wajen lalata sahihancin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon kwamishina a INEC, Mike Igini, ya buƙaci Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ɗauki tsauraran matakan diflomasiyya kan maguɗin zaɓe a Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.
Igini ya gabatar da buƙatar ne a wata wasiƙa ta buɗe wadda ya rubuta ranar 13 ga Nuwamba, 2026, ya aika wa Trump a fadar White House.

Source: Getty Images
A cikin wasiƙar, ya gabatar da wani tsari da ya kira “No Mandate Fraud”, inda ya nemi gwamnatin Amurka ta danganta hulɗar diflomasiyya da Najeriya da sahihancin zaɓen shugaban ƙasa na 2027, cewar rahoton jaridar Tribune.
Dalilin buƙatar matakin Amurka
Igini ya ce yawan maguɗin zaɓe, cin hanci da rashawa, rashin tsaro da ƙarancin ɗaukar alhakin gudanar da mulki sun raunana amincewar ’yan Najeriya ga gwamnati.
Ya kuma yi zargin cewa waɗannan matsaloli na daga cikin dalilan da ke sa ’yan Najeriya da dama neman damar rayuwa a ƙasashen waje.
A cewarsa, magance matsalolin da ke jawo ƙaura zuwa ƙasashen waje ya wuce ƙarfafa tsaron iyakoki, domin sahihin zaɓe shi ne ginshiƙin samar da shugabanci na gaskiya.
Ya ce sahihin zaɓe na taimakawa wajen ƙarfafa hukumomin gwamnati da samar da yanayin da zai ba da damar samun ci gaba mai ɗorewa.
Igini ya bayyana cewa Najeriya na da albarkatun ƙasa da na ɗan Adam da za su iya mayar da ita ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi arziki a duniya.
Sai dai ya ce tsarin zaɓen shugabanni da ake amfani da shi ya gaza samar da shugabancin da zai yi aiki domin amfanin al’umma.
Matakan da ya nemi gwamnatin Trump ta ɗauka
Tsohon kwamishinan ya buƙaci gwamnatin Trump ta haɗa matakan diflomasiyya na rigakafi, sa ido kan zaɓe daga hukumomi masu zaman kansu da kuma hukunta waɗanda aka tabbatar sun aikata laifukan zaɓe.
Ya ba da shawarar cewa Amurka ta tura wata tawaga mai manyan jami’ai domin tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu, ’yan takarar shugaban ƙasa da na gwamna, INEC, jam’iyyun siyasa da sauran hukumomin da abin ya shafa.
A cewarsa, tawagar za ta sanar da gwamnatin Najeriya matsayar Washington cewa ana buƙatar sahihin zaɓe, fafatawar siyasa cikin lumana da kuma mutunta haƙƙoƙin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Igini ya kuma nemi a kakaba takunkumi ga jami’an zaɓe da aka samu da laifin yin maguɗi da gangan, sauya sakamakon zaɓe, ƙirƙirar bayanan zaɓe na bogi da sauran manyan laifukan zaɓe.
Me yake so a yi wa jami’an INEC da shari’a?
Mike Igini ya ambaci shugaban INEC, kwamishinonin hukumar na ƙasa, kwamishinonin zaɓe na jihohi da kuma jami’an wucin gadi da ake ɗauka daga hukumomin tarayya da jami’o’i.
Ya ba da shawarar hana irin waɗannan jami’ai samun bizar Amurka, tare da yiwuwar kakaba musu takunkumin kuɗi da ƙwace kadarorinsu idan doka ta ba da damar hakan.
Dangane da ɓangaren shari’a, Igini ya nemi Amurka ta yi la’akari da matakan da suka dace kan alƙalan da aka samu da hannu wajen cin hanci da rashawa ko wasu munanan ayyuka da ke lalata adalci a harkokin zaɓe.
Sai dai ya jaddada cewa ’yancin bangaren shari’a na da matuƙar muhimmanci ga dimokuraɗiyya, amma bai kamata a yi amfani da shi a matsayin kariya ga cin hanci ko murƙushe adalcin zaɓe ba.
Haka kuma, ya nemi a ɗauki mataki kan jami’an tsaro da ake zargi da amfani da hukumomin tsaro wajen nuna goyon bayan wata jam’iyya a lokacin zaɓe.

Source: Getty Images
Trump ya yi maganar shiga aljannah
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wajen korar baƙi daga ƙasar sun yi tsauri.
Da aka tambaye shi ko yana ganin zai shiga Aljanna, shugaban ya ce shi mutum ne mai addini, don haka yana fatan hakan zai kasance.
Asali: Legit.ng