Tinubu na Saudiyya, Zanga Zangar adawa da Shi Ta Barke a Saudiyya

Tinubu na Saudiyya, Zanga Zangar adawa da Shi Ta Barke a Saudiyya

  • Daruruwan matasa maza da mata sun fito zanga-zanga a Freedom Square da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara
  • Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun sanya fararen riguna masu ɗauke da rubutun “TINUBU MUST GO” tare da rera wakokin goyon baya
  • Zanga-zangar ta haddasa cunkoson ababen hawa, yayin da har zuwa lokacin haɗa rahoton ba a bayyana dalilin gudanar da ita a hukumance ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Daruruwan matasa sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin a shahararren dandalin Freedom Square da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, lamarin da ya haddasa cunkoson ababen hawa a yankin.

Masu zanga-zangar, waɗanda suka haɗa da matasa maza da mata, sun taru ne a mahadar Freedom Square, wadda take haɗa manyan hanyoyin da ke cikin birnin Gusau.

An yi zanga zanga kan Tinubu a Zamfara
Wasu matasan da suka fito zanga-zangar adawa da Tinubu a Zamfara. Hoto: Abubakar Sadiq Sulaiman
Source: Facebook

An sanya rigunan “Tinubu Must Go”

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

A wani bidiyo da jaridar Leadership ta samu ta musamman, an ga wasu daga cikin masu zanga-zangar sanye da fararen T-shirt masu ɗauke da rubutun “TINUBU MUST GO”, wato “Tinubu ya sauka”.

An kuma ga matasan suna rera waƙoƙin nuna goyon baya yayin da suke gudanar da zanga-zangar a wajen mahadar.

Wasu daga cikin matan da suka halarta sun sanya hijabai masu launuka daban-daban, inda suka tsaya a gefen hanya suna cikin masu zanga-zangar.

Maza kuwa sun riƙa tafiya cikin ƙungiyoyi, yayin da wasu daga cikinsu ke amfani da babura a wajen gudanar da zanga-zangar.

Zanga-zangar ta haddasa cunkoson ababen hawa

Zanga-zangar ta jawo hankalin masu ababen hawa da matafiya, inda aka samu tafiyar hawainiya sakamakon yawan mutanen da suka mamaye yankin.

Masu tuka baburan adaidaita sahu, babura da motoci sun sha wahala wajen wucewa ta wurin saboda cunkoson da taron ya haifar.

Haka kuma, an ga wata mota mai ɗauke da tambarin da aka yi wa ado, wadda aka saka na’urar magana ta lasifika a kanta domin isar da saƙonni ga jama’a.

A saman motar kuwa, an ga wani mai ɗaukar bidiyo yana tsaye a kan rufinta, inda yake ɗaukar yadda abubuwan ke gudana.

Kara karanta wannan

Nasara babba: Sojoji sun kashe shugabannin ISWAP da mayaka Larabawa a Borno

Ba a bayyana dalilin zanga-zangar ba

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, masu shirya zanga-zangar ba su bayyana dalilin da ya sa suka fito ba a hukumance.

Haka kuma, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ko bayyana matsayarsu kan zanga-zangar ba a lokacin da aka haɗa rahoton.

Freedom Square ya kasance ɗaya daga cikin manyan wuraren gudanar da harkokin siyasa da zanga-zangar jama’a a Gusau tun bayan da gwamnatin jihar mai ci ta sauya masa suna.

An yi zanga zanga kan Tinubu
Matasan da suka fito zanga-zangar adawa da Tinubu a Zamfara Hoto: Abubakar Sadiq Sulaiman
Source: Facebook

Batun shigar Tinubu dakin Ka'aba

A wani labarin kuma, kun ji cewa shigar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cikin Ka'aba da ke cikin Masallacin Harami a birnin Makka na ƙasar Saudiyya ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana farin cikinsu da wannan dama da shugaban ƙasar ya samu, yayin da wasu suka nuna rashin jin daɗinsu kan yadda aka tsara shigar tasa da kuma shingayen da aka kafa a kusa da wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng