Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Yi Haramar Kai Naira Tiriliyan 200 a karkashin Tinubu

Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Yi Haramar Kai Naira Tiriliyan 200 a karkashin Tinubu

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya rubuta wa Majalisar Dattawa yana neman amincewarta a karbo bashi
  • Gwamnatin tarayya na son karɓar ƙarin bashin waje na shekarun 2026 zuwa 2027, wanda ya kusa kai N30tr a yau
  • Idan aka aro dala biliyan 20.52 da Yuro biliyan 1.05, kudin da ake bin Najeriya zai doshi Naira tiriliyan 200 kenan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon shirin karɓar bashi daga kasar waje.

Idan shugaban kasar ya samu yadda yake so, jimillar bashin Najeriya na iya haura Naira tiriliyan 200 kafin ƙarshen 2026.

Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu yana isa Beijing, China Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaba Bola Tinubu yana son aro N30tr

Idan aka yi la’akari da farashin dala a kasuwa, Daily Trust ta ce sabon bashin da ake nema ya kai kusan Naira tiriliyan 30.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Tinubu zafafan tambayoyi kan ciwo bashin $20bn da £1bn

Lissafi ya nuna bashin Najeriya na iya haura Naira tiriliyan 200 kafin ƙarshen shekara da zarar ‘yan majalisa suka amince.

Sai dai hakan zai danganta da darajar kuɗin waje, adadin bashin da aka karɓa da sauran sauye-sauyen alkaluma da za a samu.

A yanzu ana bin Najerya bashin N160tr

Bashin da gwamnati ta karbo wa Najeriya ya kai Naira tiriliyan 166.79 a ranar 30 ga Yuni, 2026, bisa bayanan Ofishin DMO.

Bayanan sun nuna cewa bashin ƙasar ya ƙaru da Naira tiriliyan 7.44 cikin watanni uku, ya tashi daga N159tr zuwa N166tr.

Ko da yanzu ana shirin shiga watan Nuwamba, har yanzu DMO ba ta fitar da bayanan bashin da aka karbo a karshen bana ba.

Bashin Najeriya zai iya kai N200tr

Amma ana hasashen cewa kudin da aka aro yana iya haura Naira tiriliyan 200 kafin ƙarshen shekara idan aka ƙaro wani bashin.

Jaridar Sun ta ce Gwamnatin Najeriya ta ci bashin N91.59tr a gida, sannan ta karbo N75.20 daga bankuna da hukumomin waje.

Kara karanta wannan

"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027

Idan aka dauki farashin dala guda kan N1500, sabon bashin da Tinubu ya nema zai jawo kudin da ake bin kasar ya kai N199.4tr.

A kiyasin shafin Worldmeter, adadin mutanen da suke Najeriya sun doshi miliyan 245.

Idan za a raba tiriliyoyin ga mutanen kasar, zai kasance zuwa karshen bana ana bin kowane ‘dan Najeriya bashin N830, 000.

Masanin tattalin arziki ya goyi bayan cin bashi

Da yake magana kan sabon shirin karɓar bashin, wani masanin tattalin arziki ya ce karɓar bashi domin iki ba bakon abu ba ne.

Dr Muhammad Bashir-Yusuf na Jami’ar Al-Hikmah da ke Ilorin ya ce muddin aka yi amfani da kuɗin bisa manufar, to babu laifi.

Ya ce gwamnatoci kan karɓi bashi daga cikin gida ko ƙasashen waje idan kuɗin da suke shirin kashewa sun fi karfin lalitarsu.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa karkatar da kuɗin daga ayyukan da aka karɓe su a yi zai rusa manufar bashin, sai a bar ƙasar da nauyi.

Talakawa a Najeriya
Talakawa a Najeriya lokacin annobar COVID-19 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

NDC ta zargi gwamnati da facaka da dukiya

An samu labari cewa jam'iyyar NDC ta caccaki Gwamnatin Bola Tinubu kan raba motocin Prado ga shugabannin matasan APC,

Kara karanta wannan

An tono yadda Sambo Dasuki ya raba biliyoyin kudin makamai zuw asusun bankuna

NDC ta ce motocin sun kai N1.0bn, ta zargi APC da fifita shanawar ’yan siyasa yayin da ’yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa.

Shugaban matasan APC, Dayo Israel ya yi wa Remi Tinubu godiya yana cewa motocin za su yi masu amfani wajen aikin kamfe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng