'Babu inda Na yi wa Jonathan Adawa': Babban Malami Ya Yi Ƙarin Haske

'Babu inda Na yi wa Jonathan Adawa': Babban Malami Ya Yi Ƙarin Haske

  • Fasto Enoch Adeboye ya musanta zargin gudanar da zanga-zanga kan Goodluck Jonathan, yana mai cewa tattakin da ya yi a 2020 na addu'a ne
  • Adeboye ya zargi wasu 'yan jarida da karkatar da gaskiya, yana mai cewa ba su binciki lokacin da kuma dalilin gudanar da tattakin ba
  • Malamin ya ce rahoton ya yi ikirarin cewa ya dauki kwalin zanga-zanga domin nuna adawa da gwamnatin tsohon shugaban kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fasto Enoch Adeboye ya musanta cewa ya gudanar da zanga-zanga kan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.

Babban limamin cocin RCCG ya ce ya dauki kwalin rubutu ne a shekarar 2020, shekaru biyar bayan Jonathan ya bar mulki.

Adeboye ya musanta adawa da mulkin Jonathan
Babban malamin Kirista, Bishop Adeboye. Hoto: Bishop Enoch Adeboye.
Source: Instagram

Fasto Enoch Adeboye ya bayyana hakan ne yayin hidimar godiya ta watan Nuwamba da cocinsa ya gudanar ranar Lahadi, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Alfarmar da shugabannin Arewa suka nema daga Tinubu saboda zaɓen Buhari

Adeboye ya zargi yan jarida

Adeboye ya zargi wasu 'yan jarida da karkatar da gaskiya, yana mai cewa ba su binciki lokacin da kuma dalilin gudanar da tattakin addu'ar ba.

Ya ce wani rahoto da aka wallafa kwanan nan ya nuna shi a matsayin mutumin da ya gudanar da zanga-zanga kan Jonathan.

Adeboye ya ce rahoton ya yi ikirarin cewa ya dauki kwalin zanga-zanga domin nuna adawa da gwamnatin tsohon shugaban kasar.

Ya bayyana cewa da farko ya yi murmushi lokacin da ya ji labarin, saboda ya san cewa zargin ba gaskiya ba ne.

Limamin ya bayyana cewa an gudanar da tattakin ne bayan shugaban cocin ya umurci dukkan rassan RCCG su yi addu'a a kusa da majami'unsu.

Ya ce:

"Gaskiya ne, na dauki kwalin rubutu. Ba zan iya musanta hakan ba. Abu ne mai muhimmanci. Tattakin addu'a ne. Mun je yin addu'a.
"Shugaban ya ce dukkan majami'u su gudanar da tattakin addu'a a kusa da wuraren ibadarsu. Wannan shi ne abin da na yi."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ba da mamaki, ya dauki alkawari shiga dazuka da afafunsa

Fasto ya musanta adawa da Jonathan
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: UGC

Yaushe Adeboye ya yi tattakin?

Adeboye ya jaddada cewa ranar da ya gudanar da tattakin ta tabbatar da cewa ba zanga-zanga ce kan gwamnatin Jonathan ba.

Faston ya zargi dan jaridar da karkatar da bayanan, yana mai cewa mutane sun amince da rahoton ba tare da tantance sahihancinsa ba.

Adeboye ya kuma tuna lokacin da ya yi karatun aikin jarida a shekarun 1960, inda ya koyi muhimmancin binciken gaskiya kafin wallafa labarai.

Ya ce:

"Na dauki kwalin ne a shekarar 2020. Jonathan ya bar shugabancin Najeriya a shekarar 2015. Na yi hakan ne shekaru biyar bayan ya bar mulki, a wa'adin Buhari na biyu.
"Amma wani dan jarida ya karkatar da maganata. Na ce na yi abin da na yi a shekarar 2015. Sai kowa ya amince da hakan."

Da yake magana kan ma'aikatan masana'antar kirkire-kirkire, Adeboye ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka amince da rahoton ba tare da bincike ba.

Kara karanta wannan

'Gyaran da Peter Obi zai yi a bangaren da Tinubu ya nakasa a Najeriya'

Ya ce:

"Ina magana ne da wadanda ke cikin masana'antar kirkire-kirkire. Babu wanda ya yi bincike."

A ranar 2 ga watan Fabrairun 2020, Adeboye ya jagoranci mambobin cocin RCCG gudanar da tattakin addu'a a Lagos domin nuna damuwarsu kan kashe-kashe da matsalar tsaro.

Tattakin ya biyo bayan shirin azumi da addu'a na kwanaki uku da kungiyar CAN ta ayyana domin neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro, cewar Tribune.

Dogara ya kare Tinubu kan tsaro

An ji cewa, tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya bayyana lokacin da matsalolin tsaro suka fara a Najeriya.

Dogara ya ce matsalolin tsaron Najeriya sun samo asali tun kafin gwamnatin Bola Tinubu, inda ya ce ta'addanci sun daɗe a ƙasar kafin shekarar 2023.

Dogara ya bayyana hakan ne a ƙarshen mako yayin bikin yaye ɗalibai karo na 16 na jami'ar, inda ɗalibai 836 suka karɓi takardun shaidar kammala karatunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.