Ubangiji Bai Fada Min Za'a Yi Zabe A 2023 Ba, Fasto Enoch Adeboye

Ubangiji Bai Fada Min Za'a Yi Zabe A 2023 Ba, Fasto Enoch Adeboye

  • Babban Faston cocin RCCG ya jefa shakku kan yiwuwan zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa
  • Malamin yace yan Najeriya fa su cika da addu'a saboda abubuwan dake faruwa yanzu sun fara saba hankali
  • Hukumar gudanar da zabe ta INEC ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa, gwamnoni da yan majalisa a rubu'in farkon 2023

Lagos - Jagoran babban cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG, Pastor Enoch Adeboye, ya bayyana cewa shi har yanzu bai tunanin zabe zai gudana a Najeriya a shekarar 2023.

Adeboye ya ce duk da cewa an saura watanni uku a yi zaben, ubangiji bai fada masa ko za'ayi zabe ko ba zai yiwu ba.

Babban faston ya bayyana hakan ne a taron 2022 Holy Ghost Service, rahoton Vanguard.

Ya baiwa yan Najeriya shawara su taimaki kansu su rike murmushi saboda matsalolin kasar nan kadai sun isa su baiwa mutum hawan jini.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

Yace:

"Ya kamata mu nemi rahamar Allah saboda abin dake faruwa a kasarmu yanzu, abin ya fara saba hankali."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba tsoro nike ba ku ba, Amma sai Allah ya yi mana rahama. Shin kun san ana Nuwamba, amma har yanzu Ubangiji ba fada min ko za'ayi zabe a shekara mai zuwa ba."
Enoch
Ubangiji Bai Fada Min Za'a Yi Zabe A 2023 Ba, Fasto Enoch Adeboye Hoto: @TheHQService
Asali: Twitter

2023: Sabuwar Na’urar BVAS da INEC ta Kawo Za ta Hana Magudin Zabe

A wani labarin kuwa, Sanata Victor Ndoma-Egba ya nuna yana goyon bayan amfani da na’urorin BVAS da hukumar INEC za tayi a zaben shekara mai zuwa.

Daily Trust ta rahoto tsohon jagora a majalisar dattawan yana cewa BVAS da sauran fasahohin zamani a za ayi amfani da su za su inganta zabe.

Victor Ndoma-Egba ya yi wannan jawabi a garin Abuja a lokacin da ‘ya ‘yan kungiyar 'APC National Integrity Movement' suka kai masa ziyara.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

Da aka kai masa ziyara har gidansa a Abuja, ‘dan siyasar ya shaidawa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC cewa cigaban da aka kawo zai canza harkar zabe.

BVAS zai taimakawa APC - Ndoma-Egba

A cewar Victor Ndoma-Egba, fasahohin da za ayi amfani da su za su taimakawa jam’iyyarsu ta APC mai mulki wajen samun galaba a zaben badi.

Jagoran na APC yace zaben 2023 zai sha ban-bam da na baya domin wadannan cigaba na fasaha da kara wayewa da masu kada kuri’a suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel