Gwamnan Kebbi Ya Kirkiro Sabbbin Masarautu, Ya Yi Nade Nade
- Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya amince da ƙirƙirar sabbin gundumomi bakwai a wasu yankunan Masarautar Zuru domin ƙarfafa hukumomin gargajiya
- Gwamnatin ta naɗa sababbin hakimai da dagatai a ƙananan hukumomin Fakai, Danko-Wasagu da Zuru
- Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ya ce an gudanar da naɗe-naɗen bisa dokar ƙananan hukumomin Jihar Kebbi ta 2008
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da ƙirƙirar sababbin gundumomi bakwai tare da naɗa hakimai da dagatai a wasu yankunan Masarautar Zuru.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa hukumomin gargajiya da inganta gudanar da mulki a matakin al'umma.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce an sanar da amincewar gwamnan ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na jihar, Garba Umar Dutsinmari, ya sanya wa hannu.
An fitar da sanarwar kirkiro sababbin gundumomin ne a Birnin Kebbi ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoban 2026.
Sunayen sababbin gundumomin da aka ƙirƙira
Sababbin gundumomin da aka sanar sun haɗa da Peni, Mahuta, Bangu, Gele, Chonoko da Ummu. Haka kuma, an ɗaukaka matsayin ƙauyen Chonoko da ke Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu zuwa gunduma.
Gwamnatin ta kuma amince da naɗa sababbin shugabannin gargajiya domin jagorantar waɗannan yankuna da wasu ƙauyuka da abin ya shafa.
A cewar sanarwar, an samar da Gundumar Peni ne daga tsohuwar Gundumar Bajida da ke Ƙaramar Hukumar Fakai, inda aka sanya hedikwatarta a Yoko.
Gwamnan ya naɗa Alhaji Ayuba Bende a matsayin sabon hakimin Gundumar Peni. Haka kuma, an ƙirƙiri gundumomin Mahuta da Bangu daga tsohuwar Gundumar Marafa, ita ma da ke Ƙaramar Hukumar Fakai.
An naɗa Alhaji Farke Anama a matsayin hakimin Mahuta, yayin da Alhaji Abubakar Wamale ya zama hakimin Bangu.
Sababbin hakimai a Fakai da Danko-Wasagu
Sanarwar ta bayyana cewa an ƙirƙiri Gundumar Gele daga tsohuwar Gundumar Bajida/Birnin Tudu da ke Ƙaramar Hukumar Fakai.
An sanya hedikwatar sabuwar gundumar a Boko, sannan aka naɗa Alhaji Ahmad D. Gele a matsayin hakiminta.
A Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu kuwa, gwamnatin ta ɗaukaka matsayin Ƙauyen Chonoko zuwa gunduma a ƙarƙashin tsohuwar Gundumar Waje.
Bayan ɗaukaka matsayin yankin, an naɗa Bamaiyi Bawada Chonoko a matsayin sabon hakimin Gundumar Chonoko.
An ƙirƙiri Gundumar Ummu, an naɗa dagatai
A Ƙaramar Hukumar Zuru, gwamnatin jihar ta ƙirƙiri Gundumar Ummu daga tsohuwar Gundumar Rafin Zuru.
A ƙarƙashin sabon tsarin, an naɗa Kabiru Chaka Diga a matsayin dagacin Sabon Garin Ummu.
Haka kuma, an naɗa Markus Yumu a matsayin dagacin Domo, Yakubu Maliki a matsayin dagacin Ugeva, Sale Oda a matsayin dagacin Chepko, yayin da Usman Idris ya zama dagacin Adhava Hanto.
Baya ga waɗannan naɗe-naɗe, Gwamna Nasir Idris ya amince da naɗa Muhammadu Danwarai a matsayin sabon dagacin Musume, da ke Ƙaramar Hukumar Zuru.
Dokar da aka yi amfani da ita
Da yake bayyana tushen dokar da aka bi wajen aiwatar da sauye-sauyen, Kwamishina Garba Umar Dutsinmari ya ce an gudanar da naɗe-naɗen da ƙirƙirar gundumomin ne bisa tanadin Dokar Ƙananan Hukumomin Jihar Kebbi ta 2008.
Kwamishinan ya kuma buƙaci sababbin sarakunan gargajiyar da aka naɗa da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da jajircewa.
Ya jaddada muhimmancin sauke nauyin da aka ɗora musu wajen gudanar da harkokin gargajiya da yi wa al'ummomin da suke jagoranta hidima.

Source: Original
Gwamnan Kebbi ya ajiye mataimakinsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya zabi tsohon Kwamishinan Kudi na jihar, Alhaji Ibrahim Augie, a matsayin sabon abokin takararsa a zaben gwamna na 2027.
Zabar kwamishinan na nufin an sauke mataimakin gwamnan mai ci, Sanata Umar Tafida, daga matsayin abokin takarar Idris a zaben 2027.
Asali: Legit.ng


