Ebola Ta Ci Gaba da Yaduwa a Najeriya, NCDC Ta Gano Karin Mutanen da Suka Kamu

Ebola Ta Ci Gaba da Yaduwa a Najeriya, NCDC Ta Gano Karin Mutanen da Suka Kamu

  • Hukumar NCDC mai kula da cututtuka masu yaduwa ta gano wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Najeriya
  • Hukumar ta kuma gano mutane 53 da suka yi mu’amala kai tsaye da waɗanda ake zargin sun kamu da cutar
  • Darakta-Janar na NCDC, Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta gano wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola.

Hukumar NCDC ta kuma gano wasu mutane 53 da suka yi mu’amala kai tsaye da waɗanda ake zargin sun kamu da cutar Ebola.

Ebola ta kara yaduwa a Najeriya
Wasu dalibai na wanke hannu lokacin Ebola Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Darakta-Janar na hukumar, Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Zargin badala: Hukumar Hisbah ta cafke fitacciyar 'yar TikTok a Kano

Ana ƙara ƙaimi wajen sa ido

Wannan sabon ci gaba ya sake jaddada muhimmancin sa ido kan masu yiwuwar kamuwa da cutar Ebola da kuma bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da su.

Hukumomin lafiya na ci gaba da ƙoƙarin gano mutanen da ka iya fuskantar haɗarin kamuwa da cutar, domin a iya sa musu ido tare da ɗaukar matakan da suka dace don hana yaɗuwarta idan an tabbatar da kamuwa.

Ku dakaci karin bayani.....

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng