Ana Jimamin Masussuka, 'Yan Bindiga Sun kai Hari Kaduna, Sun Yi Ta'addanci

Ana Jimamin Masussuka, 'Yan Bindiga Sun kai Hari Kaduna, Sun Yi Ta'addanci

  • Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari Nuru Suraj Estate da ke Millennium City a Kaduna da sanyin safiyar Talata, inda suka sace mutane
  • Wata mazauniyar yankin ta ce jami’an sojoji sun bi sawun maharan, inda suka samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sace, amma maharan sun tsere
  • Harin ya sake tayar da hankalin mazauna yankin kan matsalar tsaro, musamman yadda ake kai hare-hare a gidajen zama da al’ummomin da ke wajen birnin Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kaduna – Mazauna Nuru Suraj Estate da ke yankin Millennium City a jihar Kaduna sun shiga fargaba bayan wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari da sanyin safiyar Talata, inda suka yi awon gaba da kusan mutum shida.

Kara karanta wannan

Rashin imani: An ɗaure mutum 3 da ake zargi da sace ƙaramin yaro kuma suka kashe shi a Kano

Wata mazauniyar yankin mai suna Maman Hamid, wadda gidanta ke kusa da gidan waɗanda aka sace, ta shaida cewa maharan sun shiga gidan ne ta ƙofa ta biyu kafin su gudanar da aikin nasu.

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Vanguard ta rahoto cewa Maman Hamid ta ce lamarin ya jefa mazauna yankin cikin firgici da fargabar abin da ka iya biyo baya.

Sojoji sun bi sawun maharan

Maman Hamid ta bayyana cewa jami’an sojoji sun bi sawun waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne bayan kai harin.

Ta ce jami’an sun samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sace, duk da cewa maharan sun tsere.

Sai dai ba a tabbatar da adadin mutanen da aka kuɓutar ba, ko kuma inda waɗanda har yanzu ba a gano su ba suke, a lokacin haɗa wannan rahoto.

Hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba, yayin da rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai kan lamarin ba zuwa lokacin haɗa rahoton.

Gwamna Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani a ofis. Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

'Yan Kaduna sun suna damuwa

Sabon harin ya sake jawo hankalin jama’a kan matsalar tsaro a Millennium City, wani yanki da ke bunƙasa ta fuskar gidajen zama, amma ya sha fuskantar hare-haren masu garkuwa da mutane a shekarun baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yan bindiga sun kai hari kusa da masallacin Juma'a na jami'ar Usman Danfodio

Mazauna yankin sun sha nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa gidajen zama da al’ummomin da ke gefen birnin Kaduna.

Lamarin ya kuma ƙara nuna muhimmancin tsaurara matakan tsaro a ƙofofin shiga da fita na gidajen zama, ƙara sintiri, amfani da na’urorin sa ido da kuma gaggauta ɗaukar mataki idan an samu kiran neman agaji.

An kashe mutum 50 a Taraba

A wani labarin, kun ji cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai ƙauyen Binnari da ke jihar Taraba ya kai 50, bayan an gano wasu gawarwaki a ranar Asabar.

Maharan, waɗanda ake zargin ’yan ƙungiyoyin masu aikata laifi ne sun isa ƙauyen ne a kan babura a ranar Juma’a, inda suka kashe mutane tare da wawushe shaguna.

Wani mazaunin yankin, Bashir Mamuda Musa, ya ce an gano gawarwaki bakwai a ranar Juma’a, sannan aka gano wasu 43 a cikin kogi washegari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng