Ayarin Motocin Gwamna Ya Gamu da Hatsari har Mutum 5 Sun Mutu? Gaskiya Ta Fito

Ayarin Motocin Gwamna Ya Gamu da Hatsari har Mutum 5 Sun Mutu? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnatin Neja ta musanta rahotannin da ke cewa ayarin motocin Gwamna Mohammed Umaru Bago na cikin hatsarin ya yi ajalin mutum biyar
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja ya ce direban motar da ta yi hatsarin ma’aikacin gidan gwamnatin jihar ne
  • Gwamnatin ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da jama’a su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin yaɗa su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Gwamnatin jihar Neja ta musanta rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka wallafa cewa ayarin motocin Gwamna Mohammed Umaru Bago na cikin wani hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutum biyar.

Hatsarin ya faru ne a Gidan Magoro, a kan hanyar Minna zuwa Bida, inda wasu rahotanni suka danganta lamarin da ayarin motocin gwamnan.

Gwamna Bago.
Gwamna Mohammed Umaru Bago yana jawabi a wurin taro a jihar Neja Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Facebook

Sai dai jaridar Leadership ta ruwaito cewa syarin motocin Gwamna Bago ba ya cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

An fara gano kura kurai a shirin zaben 2027, Kwankwaso ya gargaɗi INEC

Da gaske ayarin Bago na cikin hatsarin?

Da yake mayar da martani kan rahotannin, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na jihar Neja, Hon. Obed Nuhu Nana, ya bayyana alhininsa kan hatsarin da ya yi sanadin asarar rayuka.

Amma kwamishinnsn ya jaddada cewa motocin da lamarin ya shafa ba sa cikin ayarin mai girma gwamnan.

Nuhu Nana ya ce gwamnati na son fayyace gaskiyar lamarin domin jama’a su samu sahihin bayani, maimakon a ci gaba da yaɗa rahotannin da suka danganta hatsarin da ayarin Gwamna Bago.

Yadda motar gwamnati ta yi hatsari

Ya bayyana cewa direban da hatsarin ya rutsa da shi ma’aikacin gidan gwamnatin jihar Neja ne, wanda yake dawowa daga wata tafiya tare da wasu ma’aikatan gwamnati.

A cewarsa, ma’aikatan da abin ya shafa suna karɓar magani a halin yanzu, ya ƙara da cewa motar ba ta cikin ayarin motocin da ke rakiyar gwamnan a wani aiki na hukuma a lokacin da hatsarin ya faru.

Kara karanta wannan

An farmaki yan APC yayin da Gwamna Radda ya kaddamar da kamfen a Katsina

Nuhu Nana ya ce bayanan farko da gwamnati ta samu sun nuna cewa direban ya yi tuƙi cikin ganganci, lamarin da ya kai ga faruwar hatsarin.

Gwamnatin Neja ta nuna alhini

Ya bayyana cewa gwamnati ta yi nadamar yanayin da ya haddasa asarar rayukan, yana mai jaddada cewa bai kamata a yi wasa da dokokin kiyaye haɗurra a kan hanya ba.

Kwamishinan ya ce gwamnati ta fahimci damuwar da hatsarin ya jawo a tsakanin jama’a, amma ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da sauran mutane su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yaɗa su.

Neja.
Taswirar jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya kuma yi gargaɗin cewa ya kamata a yi taka-tsantsan wajen danganta irin waɗannan al’amura da gwamna ko gwamnatin jihar ba tare da cikakken tabbaci ba.

Neja ta yi ikirarin murkushe yan bindiga

Kun ji cewa gwamnatin Neja ta ce ta kawar da ayyukan 'yan bindiga da sansanoninsu a jihar, tana danganta hare-haren da ake samu da masu shigowa daga jihohin makwabta.

Ta ce duk wata barazana ta tsaro da ake gani tana fitowa ne daga miyagun masu aikata laifuffuka lmda ke shigowa daga jihohin makwabta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262