Gwamnatin Najeriya Ta Kawo da Sabon Tsarin Yaki da Talauci
- Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da sabon tsarin haɗa ayyukan agajin jin ƙai, tallafin zamantakewa da shirye-shiryen rage talauci a Najeriya
- Ministan jin ƙai da yaƙi da talauci, Bernard Doro, ya ce tsarin zai taimaka wajen tabbatar da cewa masu rauni sun samu tallafi mai inganci
- Gwamnatin tarayya ta ce sabon tsarin zai taimaka wa iyalan da ke fuskantar matsaloli su fita daga neman agajin gaggawa zuwa dogaro da kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da wani sabon tsarin da aka ƙirƙira domin yaƙi da talauci ta hanyar haɗa ayyukan agajin jin ƙai, tallafi da shirye-shiryen rage talauci a ƙarƙashin tsari guda.
Tsarin, mai suna OHOPRS zai taimaka wajen inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin agaji da abokan hulɗar ci gaba domin tabbatar da cewa ’yan Najeriya masu rauni sun samu tallafin da ya dace.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta sauya salo, ta amince da wani tsari da talakawa za su amfana a Najeriya

Source: Facebook
Najeriya za ta yaki talauci
Punch ta wallafa cewa ministan jin ƙai da rage talauci, Dakta Bernard M. Doro, ne ya gabatar da takardar neman amincewa da tsarin ga majalisar, wadda ta amince da shi ranar Laraba.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ranar Alhamis, ta bayyana cewa OHOPRS na daga cikin muhimman ginshiƙan shirin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin fitar da miliyoyin ’yan Najeriya daga talauci.
Ma’aikatar ta bayyana cewa a baya, shirye-shiryen agajin jin ƙai da na rage talauci sun kasance suna gudana ne daban-daban.
Ta ce hakan ya haifar da maimaita wasu ayyuka, rashin kai tallafi ga wasu masu buƙata da kuma wahalar taimaka wa iyalai su daina dogaro da agajin gaggawa.
Yadda sabon tsarin zai taimaka
A cewar ma’aikatar, OHOPRS ba wani sabon shiri ne na daban kawai ba, illa wani babban sauyi da zai haɗa ayyukan tallafi a ƙarƙashin tsari guda, tare da mayar da iyalai masu buƙata cibiyar tsara ayyuka, bayar da tallafi da auna sakamakonsu.

Kara karanta wannan
Tallafin mai: ADC ta sake albishir ga Ƴan Najeriya kan shirin Atiku bayan hawa mulki
A ƙarƙashin tsarin, iyalan da rikice-rikice da sauran matsalolin gaggawa suka raba da muhallansu za su ci gaba da samun taimakon abinci, matsuguni da kula da lafiya.
The Nation ta rahoto cewa ministan ya ce za a haɗa su da shirye-shiryen tallafin zamantakewa, ilimi, koyon sana’o’i da hanyoyin samun abin dogaro da kai.

Source: Twitter
Rahoton ya ce manufar ita ce taimaka wa iyalan da ke cikin mawuyacin hali su wuce matakin dogaro da agajin gaggawa zuwa samun farfaɗowa, jure wa matsaloli da kuma dogaro da kai ta fuskar tattalin arziki.
Bayan amincewar FEC, ma’aikatar ta ce za ta yi aiki tare da hukumomin gwamnati, gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, abokan hulɗar ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki domin aiwatar da tsarin.
Atiku ya caccaki Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi watsi da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta neman amincewa don karɓar bashin dala biliyan 20.52 da Yuro biliyan 1.045.
Atiku da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta ADC sun bayyana shirin karɓar bashin a matsayin wani mataki marar tunani da zai iya jefa makomar Najeriya cikin haɗari.
Ta bakin kakakin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu, Atiku ya ce buƙatar Tinubu ta tabbatar da gargaɗin da ya yi ranar 12 ga Oktoba game da shirin karɓar bashin da ya kai dala biliyan 20.
Asali: Legit.ng