Ana Wata ga Wata: Kotu Ta Bukaci INEC Ta Sauya Dan Takarar NDC

Ana Wata ga Wata: Kotu Ta Bukaci INEC Ta Sauya Dan Takarar NDC

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta soke amincewar INEC da Ibrahim Lukman a matsayin ɗan takarar NDC a zaɓen 2027
  • Kotun ta umarci hukumar ta maye gurbin sunan Lukman da na Olumuyiwa Owadara, wanda ta ce ya lashe zaɓen fitar gwani
  • Haka kuma, rahoto ya ce kotun ta umarci hukumar INEC da Ibrahhim Lukman su biya Naira miliyan 1 a matsayin kuɗin shari’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta soke matakin hukumar INEC na sanya Ibrahim Lukman a matsayin ɗan takarar jam’iyyar NDC mai wakiltar mazaɓar Oshodi/Isolo I a zaɓen 2027 a Legas.

A hukuncin da ya yanke ranar 20 ga Oktoba, 2026, Mai Shari’a Akintayo Aluko ya umarci INEC da ta cire sunan Lukman, ta maye gurbinsa da Olumuyiwa Owadara, wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar da aka gudanar ranar 29 ga Mayu.

Kara karanta wannan

An tono yadda Sambo Dasuki ya raba biliyoyin kudin makamai zuw asusun bankuna

Amupitan a wajen wani taro
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa kotun ta kuma umarci INEC da Lukman su biya Naira miliyan 1 a matsayin kuɗin shari’a.

Kotu ta ce Owadara ya lashe zaɓe

Mai Shari’a Aluko ya bayyana cewa rahoton sa ido na INEC kan zaɓen fitar da gwani ya nuna cewa Owadara ne ya samu mafi yawan ƙuri’un da aka kada bisa doka.

Kotun ta ce duk da cewa hukumar ta sanya ido kan zaɓen, daga baya ta wallafa sunan Lukman a matsayin ɗan takarar NDC a ranar 1 ga Agusta, ba tare da sanya sunan Owadara ba.

NDC ta shaida wa kotun cewa ba ta gudanar da wani zaɓen fidda gwani na daban a wannan mazaɓa ba, kuma Lukman bai shiga zaɓen da aka gudanar ba.

Owadara kuwa ya bayyana cewa ya cika takardun neman tsayawa takara kuma an miƙa su ga hukumar zaɓe.

Aluko ya ce babu wani dalili na doka da zai ba INEC damar wallafa sunan Lukman a matsayin ɗan takarar jam’iyyar, kasancewar bai shiga zaɓen fitar da gwani ba.

Kara karanta wannan

2027: Bayan gyare gyare INEC za ta fitar da sabon jerin 'yan takara

Bayanin INEC a kotu

A lokacin shari’ar, INEC ta kare kanta da cewa ta wallafa sunayen ’yan takarar da jam’iyyun siyasa suka ɗaura a shafinta.

Sai dai alkalin ya ƙi amincewa da wannan hujja, yana mai cewa hukumar ba ta gabatar da sahihiyar shaida da za ta tabbatar da ikirarinta ba.

Kotun ta kuma bayyana cewa NDC ta musanta aika sunan Lukman ga INEC, inda ta zargi hukumar da ƙoƙarin ɗaura mata ɗan takara ba tare da bin ƙa’ida ba.

Wajen zabe a jihar Osun
Yadda aka kirga kuri'u a zaben Osunna 2026. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Bayani INEC kan 'yan takara

A wani labarin, mun ruwaito cewa INEC za ta wallafa sabon jerin ’yan takarar zaɓen 2027 bayan kammala nazarin jerin sunayen da ta fitar a baya.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ne ya bayyana hakan a Gombe yayin ganawarsa da ma’aikatan INEC daga shiyyar Arewa maso Gabas.

Ya ce an gudanar da bitar ne domin magance korafe-korafe kan kuskuren rubuta sunaye da kuma samun mutum ɗaya a jerin ’yan takarar fiye da ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng