Gwamna Ya ba Matarsa Kyautar da Ta Bata Mamaki, Ya Sumbace Ta a Tsakiyar Taro

Gwamna Ya ba Matarsa Kyautar da Ta Bata Mamaki, Ya Sumbace Ta a Tsakiyar Taro

  • Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ba matarsa, Ibijoke, mamaki da kyautar furanni kafin su sumbaci juna a wajen taron mata na ƙasa karo na 26
  • Lamarin ya faru ne yayin bikin buɗe taron da ƙungiyar matan jami’an gwamnatin jihar Legas (COWLSO) ta shirya
  • Bidiyon nuna soyayyar ma’auratan ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda mutane suka ga yadda gwamnan ya girmama matarsa a bainar jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ba matarsa, Ibijoke Sanwo-Olu, mamaki ta hanyar ba ta kyautar furanni ba tareda ta yi tsammani ba.

An ce bayan kyautar furannin, Gwamna Sanwo-Olu ya kuma sumbaci uwar gidanss a wajen bikin buɗe taron mata na ƙasa karo na 26 da aka gudanar a Legas.

Legas.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu yana mika wa matarsa kyautar furanni a wurin taron mata na kasa karo na 26 Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Source: Facebook

Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata yayin taron da ƙungiyar matan jami’an gwamnatin jihar Legas (COWLSO) ta shirya.

Kara karanta wannan

"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027

Gwamna ya sumbaci matarsa

An ɗauki wannan lokaci a wani bidiyo da ya bazu a intanet, inda aka ga gwamnan yana nuna ƙauna da girmamawa ga matarsa a gaban mahalarta taron.

Sanwo-Olu ya miƙa wa matarsa furannin ne yayin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron, wanda ya haɗa mata da shugabanni domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙarfafa mata, jagoranci da kuma gina kyakkyawar makoma.

Yayin miƙa furannin, gwamnan ya bayyana cewa yana son nuna godiya da girmamawa ga matarsa a madadin ƙungiyar COWLSO da kuma dukkan mutanen da ke daraja kyawawan ɗabi’u.

“A madadin COWLSO da duk wani abu na mutunci, muna son mu nuna godiyarmu gare ki, muna son mu girmama ki,” in ji Sanwo-Olu.

Bayan haka, ma’auratan sun sumbaci juna yayin da ake kunna shahararriyar waƙar mawakin Najeriya, 2Baba, mai suna African Queen.

Waƙar, wadda ta shahara wajen yabon mace da nuna ƙauna, ta ƙara jan hankalin mahalarta taron a lokacin da ma’auratan suka nuna soyayyarsu a bainar jama’a.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

Bidiyon ya yaɗu a intanet

Bayan faruwar lamarin, bidiyon ya fara yaɗuwa a kafafen sada zumunta, inda masu amfani da su suka samu damar kallon yadda gwamnan ya ba matarsa furanni tare da nuna mata ƙauna a wajen taron.

Gwamnan Legas.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a wurin bude taron mata na kasa karo na 26 Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Source: Facebook

Sai dai babban abin da aka gani a bidiyon shi ne yadda Sanwo-Olu ya yi amfani da damar taron wajen nuna godiya da girmamawa ga matarsa, kafin suka raba wannan ɗan lokaci na soyayya a gaban mahalarta.

Taron mata na ƙasa karo na 26 ya samu halartar mata da shugabanni domin tattaunawa da gudanar da ayyukan da suka mayar da hankali kan ƙarfafa gwiwar mata.

Gwamna Sanwo-Olu ya taɓo cire tallafi

Kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya ce jihohi da kananan hukumomi sun samu karin kudaden shiga bayan cire tallafin man fetur.

Sai dai ya ce alhakin yadda za a yi amfani da kudaden yanzu ya rataya ne a wuyan gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262