Tsohon Gwamna Bafarawa Ya Kafa Sharadin Yi wa Tinubu Kamfen a 2027
- Tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya ce zai yi wa Shugaba Bola Tinubu kamfen idan ya kawo ƙarshen matsalar tsaro a Arewa kafin zaɓen 2027
- Bafarawa ya ce dawo da zaman lafiya zai bai wa manoma damar komawa gonakinsu ba tare da fargabar hare-haren ’yan bindiga ba
- Ya kuma buƙaci ’yan siyasar Arewa su haɗa kai wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa ya fi dacewa a yi amfani da kuɗin kamfen wajen taimaka wa al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya ce a shirye yake ya jagoranci tawagar kamfen ɗin Shugaba Bola Tinubu idan ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar yankin Arewa kafin babban zaɓen 2027.
Ya ce goyon bayansa ga Tinubu zai dogara ne da yadda gwamnatin za ta dawo da zaman lafiya, musamman ta yadda manoma za su iya komawa gonakinsu su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoron hare-hare ba.

Source: Twitter
Bafarawa, wanda ya jagoranci jihar Sokoto daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan rediyon RFI Hausa.
Sharadin Bafarawa ga Tinubu
Tsohon gwamnan ya ce har yanzu Tinubu yana da damar magance matsalar tsaro a sauran watannin da suka rage kafin zaɓen 2027.
Ya bayyana cewa idan shugaban ya yi nasarar dawo da zaman lafiya, zai iya fita da kansa ya yi masa kamfen tare da goyon bayan sake zaɓensa.
Daily Trust ta rahoto Bafarawa ya ce:
“Daga yanzu har zuwa lokacin zaɓe, zan iya yi wa Tinubu kamfen da kaina saboda abu guda: idan ya magance matsalar tsaron da ke damun al’ummarmu, wallahi zan zaɓe shi.”
A cewarsa, abin da al’ummar Arewa suka fi buƙata a halin yanzu shi ne tsaro da damar gudanar da harkokin rayuwarsu, ba kashe kuɗi wajen kamfen ba.

Source: Facebook
Abin da ya ce kan naɗin Yari
Da yake magana kan naɗin Sanata Abdulaziz Yari a matsayin darakta-janar na kamfen ɗin Tinubu, Bafarawa ya ce bai ga laifin tsohon gwamnan Zamfara ba da ya amince da wannan muƙami.
Ya bayyana aikin a matsayin hidimar ƙasa, yana mai cewa Yari ɗan Najeriya ne, zaɓaɓɓen sanata kuma mamba a jam’iyyar APC, don haka yana da ’yancin karɓar wannan nauyi.
Sai dai Bafarawa ya jaddada cewa naɗin Yari ba ya tabbatar da cewa Tinubu zai yi nasara ko kuma ya sha kaye a zaɓen.
Obi ya caccaki Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya kamata ya bar mulki a shekarar 2027.
Obi ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin yayin ƙaddamar da majalisar kamfen na ƙasa ta jam’iyyar NDC, inda ya ce Najeriya na fuskantar matsala a ƙarƙashin jagorancin Tinubu.
Ya ce abubuwa da dama a ƙasar na taɓarɓarewa, yana mai cewa tattaunawar da suka yi da mutane a sassa daban-daban na Najeriya ta nuna cewa suna son sabon shugabanci.
Asali: Legit.ng

