DSS Ta Cafke Mai Goyon Bayan Atiku kan Zargin Yada Karya a kan Tinubu
- Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da Mubarak Abdullahi, wanda aka fi sani da Sardaunan Samari, bisa zargin yaɗa wata wasiƙar ƙarya da aka jingina wa Shugaba Bola Tinubu
- An kama wanda ake zargin a ranar 28 ga Satumban 2026 bayan ya wallafa takardar a shafinsa na Facebook tare da rubuta cewa “Atiku na zuwa”
- DSS ta shigar da tuhume-tuhume guda uku a kansa a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, bayan kotun majistare ta bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali na Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da wani magoyin bayan Atiku Abubakar, mai suna Mubarak Abdullahi, wanda aka fi sani da Sardaunan Samari.
Rahotanni sun nuna cewa an kama shi ne bisa zargin yaɗa wata wasiƙar ƙarya da aka ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika wa shugaban Amurka.

Kara karanta wannan
Rashin imani: An ɗaure mutum 3 da ake zargi da sace ƙaramin yaro kuma suka kashe shi a Kano

Source: Facebook
Mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Yadda aka kama Mubarak
A cewar Onanuga, an kama Mubarak a ranar 28 ga Satumba bayan ya wallafa takardar da ake zargin ƙarya ce a shafinsa na Facebook.
An ce takardar tana nuna cewa Tinubu ya rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban Amurka, yayin da wanda ake zargin ya wallafa ta tare da taken “ATIKU IS COMING”, ma’ana Atiku na zuwa.
Rahoton ya bayyana Mubarak a matsayin mai goyon bayan Atiku Abubakar, wanda ya amince wa masu bincike cewa ya wallafa takardar, tare da neman afuwa kan abin da ya aikata.
Sai dai Onanuga ya ce neman afuwar bai hana ɗaukar matakin shari’a a kansa ba.
Kotu ta yi umarnin a tsare shi
Bayan kama shi, an gurfanar da Mubarak a gaban Kotun Majistare mai lamba 10 da ke Kabala Doki, a jihar Kaduna.
Kotun ta bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali na Najeriya da ke Kaduna.
Haka kuma, DSS ta shigar da tuhume-tuhume guda uku a kansa a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, waɗanda suka shafi laifuffukan intanet da ɓata suna.

Source: Facebook
Sai dai har yanzu ba a sanya ranar da za a fara gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya kan waɗannan tuhume-tuhume ba.
FIB ta kama mutane a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta kama mutane tara a Najeriya yayin wani samame da aka gudanar kan ƙungiyoyin masu aikata laifi.
Daraktan FBI, Kash Patel, ya bayyana cewa jami’an sun kuma ƙwace na’urorin lantarki guda 53 tare da gano kuɗin da suka kai dala miliyan 11 da ka iya yiwuwa a daskarar da su a ƙasashe daban-daban.
Patel ya ce an gudanar da aikin mai suna Operation Blackout ne domin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifi a intanet da ke damfarar Amurkawa.
Asali: Legit.ng
