Abu na Mu: Hadimin Gwamna Abba Ya Nada Dansa Shirgegen Mukami a Ofishinsa

Abu na Mu: Hadimin Gwamna Abba Ya Nada Dansa Shirgegen Mukami a Ofishinsa

  • Ahmad Aruwa ya nada dansa, Aliyu Ahmed, a matsayin shugaban ma’aikatansa bayan sanar da nade-nade guda biyar ranar 27 ga Oktoba, 2026.
  • Sauran wadanda aka nada sun hada da Habibu Liman, Adamu Mai Salati, Isa Ahmed Don da Musa Muhammad Daurawa
  • Aruwa ya yi alkawarin biyayya da jajircewa wajen yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf aiki, tare da tallafa wa manufofin gwamnatin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Ahmad Aruwa, mai ba Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, shawara kan yada labarai, ya nada dansa, Aliyu Ahmed, a matsayin shugaban ma’aikatansa.

Aliyu Ahmed na cikin mutane biyar da aka sanar da nadinsu a ranar Talata, 27 ga Oktoban shekarar 2026.

Ahmad Aruwa ya ba dansa mukami
Ahmad Aruwa na mika takardar nadi ga dansa Hoto: Ahmad Aruwa SA
Source: Facebook

Ahmad Aruwa ya sanar da nade-naden ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Talata, 27 ga watan Oktoban 2027.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya gano abin da ya haddasa rashin tsaro, ya samo hanyar magance matsalar

Aruwa ya ba dansa mukami

Sauran wadanda aka nada sun hada da Habibu Liman a matsayin sakatare na musamman, Adamu Mai Salati a matsayin jami’in kula da harkokin ladabi da tarba.

Hakazaila akwai Ahmed Don a matsayin Darakta-Janar na yada labarai da sadarwa, da Musa Muhammad Daurawa a matsayin mataimaki na musamman.

Nade-naden dai na zuwa ne bayan Ahmad Aruwa ya karbi takardarsa ta fara aiki a matsayin hadimin Gwamna Abba.

Aruwa zai yi biyayya ga Gwamna Abba

Aruwa ya yi alkawarin biyayya ga Gwamna Abba Yusuf Da yake jawabi bayan karbar takardar nadinsa, Aruwa ya yi alkawarin tabbatar da cewa ya cancanci amincewar da gwamnan ya nuna masa.

Ya ce zai gudanar da aikinsa cikin sadaukarwa, biyayya da jajircewa wajen sauke nauyin da aka dora masa.

Aruwa ya jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ne jagoransa a siyasa, yana mai bayyana cikakken goyon bayansa ga gwamnan.

Kara karanta wannan

Isa Ashiru ya fito da gaskiyar zance bisa zargin ya fallasa El Rufai kan rashin tsaro a Kaduna

"Bari na bayyana karara cewa jagorana shi ne Abba, ubangidana a siyasa shi ne Abba, jam’iyyata ta siyasa kuma ita ce Abba.” In ji shi.

Ya kara da cewa zai yi aiki tukuru domin tallafa wa nasarar gwamnan a dukkan matakai.

Ya yaba wa tawagarsa ta yada labarai

Aruwa ya kuma yaba wa tawagarsa ta yada labarai bisa goyon baya da jajircewar da suke nunawa wajen gudanar da ayyukansu.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa za su ci gaba da aiki tare domin wayar da kan jama’a game da manufofi, shirye-shirye da nasarorin gwamnatin Jihar Kano.

Aruwa ya nuna cewa hadin kai da jajircewa za su taimaka wajen inganta yadda tawagarsa ke gudanar da ayyukanta da kuma isar da bayanai game da ayyukan gwamnatin jihar ga al’umma.

Ahmad Aruwa ya samu mukami
Ahmad Aruwa dauke da takardar nadin da aka yi masa Hoto: Ahmad Aruwa SA
Source: Facebook

Kotu ta yi hukunci kan yi wa Abba barazana

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci a ƙarar da aka shigar kan wani matashi, Sanusi Dankaka, wanda ake zargi da barazanar yaɗa bidiyo da hotunan tsiraicin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kotun tarayya ta kori karar gaba daya bayan bangaren masu kara sun sanar da janyewa, kuma lauyan wanda ake tuhuma bai yi musu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng