Kasashen Musulmi 2 na Neman Rincabewa bayan kai Mugun Farmaki
- Sojojin Jordan sun kai hare-haren sama a kudancin Siriya, inda hukumomin ƙasar suka ce mutane akalla bakwai sun mutu, ciki har da yara uku da mace
- Harin na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya kan harin da aka kai wa masu zaman makoki a wani coci a Jordan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum akalla tara
- Bayan harin, Siriya ta rufe babbar mashigar iyakar ƙasashen biyu, yayin da ta musanta cewa ta yi haɗin gwiwa da Jordan wajen kai hare-haren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jordan – Sojojin Jordan sun kai hare-haren sama a kudancin Siriya domin ɗaukar matakin ramuwar gayya kan harin da wasu ’yan bindiga suka kai wa masu zaman makoki a wani coci a Jordan a makon da ya gabata.
Hukumomin Siriya sun bayyana cewa hare-haren da aka kai a ranar Litinin sun kashe mutane akalla bakwai, ciki har da yara uku da mace, tare da jikkata wasu.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa harin ya kuma sa hukumomin Siriya rufe babbar mashigar iyakar ƙasar da Jordan, lamarin da ya dakatar da zirga-zirgar mutane da kayayyaki tsakanin ƙasashen biyu.
Jordan ta tabbatar da kai harin
Rundunar sojojin Jordan ta bayyana cewa ta kai hare-haren ne kan wuraren ɓuya na ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a kudu maso gabashin Siriya.
Ta ce matakin martani ne ga harin da aka kai wa wani coci a yankin Karak na Jordan a ranar Juma’a, inda aka kashe mutum akalla tara tare da jikkata wasu da dama.
Rundunar sojin Jordan ta kuma yi iƙirarin cewa an kai hare-haren ne bisa haɗin gwiwa da gwamnatin Siriya.
A cewar rundunar, hare-haren sun yi sanadin mutuwa da jikkatar mambobin ƙungiyoyin da ta kira ’yan ta’adda, tare da lalata wasu motocinsu.
Sai dai gwamnatin Siriya ta musanta wannan iƙirari, tana mai cewa ba a sanar da ita ba kafin kai hare-haren.
Mutane bakwai sun mutu
BBC ta rahoto cewa hukumar agajin gaggawa ta Siriya ta ce hare-haren sun shafi wurare akalla huɗu a yankunan karkara na lardunan Deraa da Suweyda a yammacin ranar Litinin.
Ta bayyana cewa jami’anta sun gano gawarwakin mutum bakwai, waɗanda suka haɗa da maza uku, mace ɗaya da yara uku.
Mutane biyar da suka mutu, wato namiji, mace da yara uku, ’yan gida ɗaya ne da harin ya rutsa da su a wani tanti da ke ƙauyen Al-Tai a lardin Deraa.
Hukumar ta ce wasu mutum uku daga iyalin, ciki har da yaro, sun jikkata a harin.
Wani harin ya kashe wani dattijo mai shekara 80 a yankin Al Shayyah, shi ma a lardin Deraa.

Source: Getty Images
Gwamnatin Siriya ta bayyana cewa ba a yi mata sanarwa ko tuntuba kafin gudanar da hare-haren sojojin Jordan ba.
An yi taron tsaro a Iran
A wani labarin, kun ji cewa Saudiyya da ƙawayenta sun tura manyan jami’an tsaro zuwa Iran a ranar Litinin domin tattaunawa kan yadda za a rage rikicin da ke barazanar ƙara dagula zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Rashin imani: An ɗaure mutum 3 da ake zargi da sace ƙaramin yaro kuma suka kashe shi a Kano
Tawagar ta haɗa da babban hafsan sojojin Pakistan, Asim Munir, da shugaban leƙen asirin Turkiyya, Ibrahim Kalin, tare da Ministan Tsaron Saudiyya, Yarima Khalid bin Salman.
Rahoto ya nuna cewa sun gana da manyan jami’an Iran, ciki har da shugaban tsaron ƙasa, Mohsen Rezaei, da Shugaba Masoud Pezeshkian.
Asali: Legit.ng

