Rashin Imani: An Daure Mutum 3 da Ake Zargi da Sace Karamin Yaro Kuma Suka Kashe Shi a Kano

Rashin Imani: An Daure Mutum 3 da Ake Zargi da Sace Karamin Yaro Kuma Suka Kashe Shi a Kano

  • Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare mutane uku kan zargin garkuwa da kashe wani yaro mai suna Aliyu Haidar
  • Ana zargin waɗanda ake tuhuma da haɗa baki wajen neman kuɗin fansa na Naira miliyan biyu kafin su kashe yaron
  • Kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar 4 ga Disamba, 2026, domin fara sauraron shaidun da za su bayar da shaida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare mutane uku a gidan yari kan zargin sacewa da kashe wani yaro mai suna Aliyu Haidar a ƙauyen Gobirawa da ke Ƙaramar Hukumar Rano.

Waɗanda ake tuhuma sun haɗa da Hajara Sani, Hayatullah Armayau da Jibin Ado. Ana tuhumarsu da haɗin baki wajen aikata laifi, garkuwa da mutane da kuma kisan kai.

Kara karanta wannan

An fitar da bidiyon El Rufa'i ya sumbaci matarsa a harabar kotu

Kotu.
Gudumar da ake amfani da ita yayin shari'a a kotunan Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Daily Trust ta ruwaito cewa lauyoyi masu gabatar da ƙara, Barista Lamido Abba Soran Dinki da Iliyasu Ibrahim, ne suka gabatar da mutanen ukun a gaban kotun domin amsa tuhume-tuhumen da ake yi musu.

An tura wadanda ake zargi kurkuku

Bayan an karanta musu tuhume-tuhumen, dukkan waɗanda ake tuhuma sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da su.

Bayan sauraron bayanan da aka gabatar a gabanta, kotun ta bayar da umarnin tsare su a gidan yari yayin da ake jiran ci gaba da shari’ar.

Haka kuma, ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 4 ga Disamba, 2026, domin fara sauraron shaidun da za su bayar da shaida a kan lamarin.

Yadda aka yi zargin sace yaron

A cewar masu gabatar da ƙara, Hajara Sani, wadda ake zargin tana aiki a gidan iyalan marigayin, ita ce ta sace Aliyu Haidar tare da kai shi wajen sauran waɗanda ake tuhuma, wato Hayatullah Armayau da Jibin Ado.

Kara karanta wannan

Mutane sun fada kogi yayin gudun tsira daga 'yan bindiga, an samu gawa 50

Masu gabatar da ƙarar sun yi zargin cewa mutanen ukun sun haɗa baki wajen neman kuɗin fansa na Naira miliyan biyu daga iyalan yaron domin a sake shi.

Sai dai, bisa bayanin masu gabatar da ƙara, an kasa biyan kuɗin fansar da ake nema, lamarin da ake zargin ya kai ga kashe yaron.

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Zargin ya haɗa da sace yaron, neman kuɗin fansa da kuma kisan da ake zargin waɗanda ake tuhuma sun aikata bayan ba a biya kuɗin ba.

Sai dai har yanzu waɗannan zarge-zarge ne da ake buƙatar tabbatar da su a gaban kotu kafin yanke hukunci.

Kotun ta sanya ranar 4 ga Disamba, 2026, domin fara sauraron shaidun da za su taimaka wajen fayyace yadda lamarin ya faru da kuma tantance zarge-zargen da ake yi wa waɗanda ake tuhuma.

Kotu ta hukunta wanda ya kashe abokinsa

Kun ji cewa an yanke wa Ayuba Sani Tumfafi hukuncin daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali bisa kashe abokinsa, Ibrahim Dan Larai.

Hukuncin ya biyo bayan wani saɓani da ya ɓarke tsakanin Ayuba da marigayin kan tashi domin yin sallar Asuba, wanda daga baya ya kai ga mutuwar Ibrahim.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262