Manyan Saudiyya da na Kasashen Musulmi 2 Sun Tafi Iran Taron Tsaro
- Jami’an tsaro daga Saudiyya, Turkiyya da Pakistan za su gana da takwarorinsu na Iran a birnin Tehran domin tattauna batutuwan tsaron yankin
- Tattaunawar na zuwa ne yayin da hare-haren ‘yan Houthi na Yemen kan Saudiyya ke ƙara tsananta, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a yankin
- Ƙasashen uku na ƙoƙarin rage tashin hankali ta hanyar diflomasiyya, yayin da Pakistan ke taka rawa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jami’an tsaro daga ƙasashen Saudiyya, Turkiyya da Pakistan za su je birnin Tehran na ƙasar Iran domin gudanar da tattaunawa kan tsaro da yadda za a rage tashin hankalin da ke addabar yankin.
Jami’an ƙasashen uku na cikin waɗanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro ta Makka, wadda ta tanadi cewa harin da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen mambobin ana ɗaukarsa a matsayin hari kan sauran ƙasashen.

Source: Getty Images
Jami’an Saudi za su halarci taron
Al Jazeera ta wallafa cewa mataimakin sakataren Majalisar Tsaron Iran, Ali Bagheri Kani, ya ce ministan tsaron Saudiyya, Khalid bin Salman Al Saud, shugaban rundunar sojin Pakistan, Asim Munir za su hallara.
Haka zalika shugaban hukumar leƙen asirin Turkiyya, Ibrahim Kalin, zai halarci taron a yau Litinin.
Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Mohsen Rezaei, ne zai jagoranci tawagar Iran.
Bagheri Kani ya bayyana cewa tattaunawar za ta iya taimaka wa ƙasashen yankin wajen ɗaukar matakai masu tasiri domin samar da tsaro bisa haɗin gwiwar ƙasashen yankin da kansu.
Rahoton Bloomberg ya nuna cewa Mataimakin ministan Saudiyya mai kula da hulɗar jama'a ta ƙasa da ƙasa, Rayed Krimly, shi ma ya tabbatar da taron.
Ya ce ziyarar wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙasashen kawancen na rage tashin hankali tsakanin ɓangarorin da ke cikin rikicin, tare da ƙarfafa tattaunawa da hanyoyin diflomasiyya.

Source: Getty Images
Hare-haren Houthi sun zafafa
Tattaunawar za ta kasance ganawa ta farko a babban matakin shugabanci tsakanin Iran da dukkan mambobin kawancen tun bayan da mayaƙan Houthi na Yemen suka ƙara kai hare-hare kan Saudiyya a watan da ya gabata.
A ranar Lahadi, Saudiyya ta ce ta tare wasu makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa da aka harba yayin da rikici da Houthi ke ci gaba.
A farkon wannan watan, ministocin ƙasashen kawancen sun gudanar da taron gaggawa a Riyadh, inda suka amince da tabbatar da saurin tura sojoji da kayan aikin yaƙi zuwa Saudiyya domin ƙarfafa tsaronta.
Iran ba ta kai hari Saudi ba
A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta musanta zargin cewa tana da hannu a hare-haren da mayaƙan Houthi na Yemen ke kai wa Saudiyya.
Bayanin Iran ya biyo bayan zargin da wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ya yi cewa Tehran ta ƙarfafa Houthi su tsananta hare-harensu kan ƙasar.
Tun bayan sake tsananta yakin basasar Yemen a watan Yuli, mayaƙan Houthi masu alaƙa da Iran sun kai hare-hare kan wasu wuraren Saudiyya, ciki har da jiragen dakon mai a Bahar Maliya.
Asali: Legit.ng

