Ana Shirin Zaɓe, Ƴan Isra'ila Sun Cika Tituna Suna Zanga Zangar Ƙin Netanyahu
- Dubban Isra’ilawa ne suka fito zanga-zanga a Tel Aviv domin nuna adawa da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu a ranar Asabar
- Masu zanga-zangar sun bukaci kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba, 2023, da abubuwan da suka gabace shi
- A cewar hukumomin Isra’ila, mayakan Hamas da wasu ƙungiyoyin Falasɗinawa sun kashe mutum kusan 1,200, tare da yin garkuwa da sama da 250
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Isra’ila a yammacin ranar Asabar domin nuna adawa da gwamnatin kasar.
Masu zanga-zangar sun fito ne domin nuna adawa da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu ana shirin zaɓe.

Source: Facebook
Rahoton Al Jazeera ya ce hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin gudanar da zaben kasar wanda ake ganin zai yi zafi kenan.
Yadda ake musgunawa Falasɗinawa
An zargi 'yan share wuri zauna da kona masallatai biyu da kuma motoci da gonaki a yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.
Hare-haren sun zo ne kwana biyu bayan wani rikici tsakanin Isralawan da Falasɗinawa ya yi sanadiyyar mutuwar Falasɗinawa huɗu da Isra’ilawa biyu.
Rikicin Isra'ilawa ya ƙara tsananta yanayin tsaro a yankin, yayin da hare-haren da ake kai wa Falasɗinawa ke ƙaruwa.

Source: Getty Images
Masu zanga-zanga sun dura kan gwamnatin Isra'ila
A wani gangami da aka gudanar a birnin Tel Aviv da ke gabar teku, tsofaffin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma iyalan waɗanda suka mutu sun bukaci kafa kwamitin bincike na gwamnati kan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
A cewar alkaluman hukumomin Isra’ila, mayakan Hamas da wasu ƙungiyoyin Falasɗinawa masu tsattsauran ra’ayi sun kashe kusan mutum 1,200 a Isra’ila.
Haka kuma, sun yi garkuwa da mutane sama da 250, inda suka kai su yankin Zirin Gaza.
Masu zanga-zangar sun soki shugabannin gwamnati kai tsaye, tare da rera wasu taken zanga-zanga, ciki har da:
“Ba za mu manta ba, ba za mu yafe ba.”
Zanga-zangar ta gudana ne gabanin zaɓen majalisar dokokin Isra’ila da aka tsara yi a ranar 27 ga Oktoba, 2026, cewar CNN.
Masu zanga-zangar sun bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan harin na 7 ga Oktoba, 2023, da abubuwan da suka kai ga faruwarsa.
Ana zargin Falasɗinawa sun kashe sojojin Isra'ila
Mun ba ku rahoton cewa an kashe sojojin Isra’ila biyu a wani harin harbe-harbe da wasu da ake zargin Falasɗinawa ne suka kai kan shingen binciken sojoji.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya umarci sojoji su shirya killace Yammacin Kogin Jordan gaba ɗaya.
Harin ya ƙara tayar da hankali gabanin zaɓen Isra’ila, inda wasu ministoci masu tsattsauran ra’ayi suka buƙaci ƙarin matakan soji.
Asali: Legit.ng

