Sarki Sanusi II Ya Sanar da Rasuwar Babban Basarake a Kano
- Masarautar Kano ta sanar da rasuwar Alhaji Ibrahim Sani Gaya, Ubandoman Kano kuma Hakimin Takai, wanda ya rasu yana da shekaru 80 a duniya
- Sanarwar da mai martaba Muhammadu Sanusi II ya fitar ta ce za a gudanar da jana'izar marigayin ranar Litinin da misalin karfe 9:00 na safe a gidansa da ke garin Gaya
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, musamman Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, da sauran al'ummar Gaya bisa wannan babban rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Masarautar Kano ta sanar da rasuwar Ubandoman Kano kuma Hakimin Takai, Alhaji Ibrahim Sani Gaya wanda Allah Ya yi wa rasuwa yana da shekaru 80 a duniya.
Sanarwar rasuwar ta fito ne daga mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II, inda aka bayyana alhini da jimamin da masarautar ke ciki sakamakon wannan babban rashi.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da rasuwar hakimin ne a wata sanarwa da aka fitar a shafin mai martaba Muhammadu Sanusi II na Facebook a ranar Lahadi, 11 ga Oktoban 2026.
Yaushe za a yi jana'izar basaraken?
A sanarwar, masarautar ta bayyana cewa za a gudanar da jana'izar marigayin ranar Litinin, 12 ga Okotban 2026 da misalin karfe 9:00 na safe.
Rahotanni sun tabbatar da cewa za a gudanar da sallar jana'izar ne a gidansa da ke garin Gaya.
Masarautar ta kuma yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya ji kansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya kuma sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.
Bashir Ahmad ya yi ta'aziyya
Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, musamman Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, 'yan uwa da daukacin al'ummar Gaya.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Bashir Ahmad ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan marigayin da al'ummar da ya yi wa hidima.
Ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya ji kansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, tare da bai wa iyalansa da duk wadanda wannan rashi ya shafa hakurin jurewa.
Tsohon hadimin shuaban kasar ya kuma roki Allah Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomar marigayin.

Source: Original
Ana sa ran 'yan uwa da abokan arziki, 'yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a jihar Kano da kewaye za su hallara jana'izar marigayin a yau Litinin.
Ciyaman ya rasu a Adamawa
A wani labarin, kun ji cewa shugaban karamar hukumar Fufore ta jihar Adamawa, Hon. Dr. Yahaya Sa'idu, ya rasu bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Jami'in yada labarai na karamar hukumar, Ahmed B. Yusha'u, ne ya bayyana rasuwar a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar Asabar a Yola.
Rasuwar ta jefa karamar hukumar da jihar cikin jimami, musamman ganin cewa ta zo ne wata 18 bayan mutuwar magabacinsa, Hon. Shaibu Basbas, wanda shi ma ya rasu yana kan mukami.
Asali: Legit.ng

