Tinubu Ya Kwantar da Hankulan Yan Najeriya kan Yadda Za a Gudanar da Zaben 2027
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani yunkurin haddasa tashin hankali ko tsoratar da masu kada kuri’a a zaben 2027 ba
- Ya bukaci ’yan Najeriya su mallaki katin zabe na PVC tare da amfani da shi wajen zaben shugabannin da suke so
- Shugaban ya kuma sanar da sababbin matakan shawo kan matsalar rashin tsaro da ta dade tana addabar jihar Filato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jos, Nigeria - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ’yan kasar cewa za a gudanar da babban zaben shekarar 2027 cikin zaman lafiya.
Tinubu ya gargadi mutane da kungiyoyin da ke shirin haddasa tashin hankali ko tsoratar da masu kada kuri’a cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani yunkuri na kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya ba.

Source: Facebook
The Nation ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin gangamin yakin neman zabensa na shugaban kasa karkashin APC a Jos, babban birnin jihar Filato.
Tinubu ya ba yan Najeriya tabbaci
Shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da samar da isasshen tsaro domin bai wa ’yan kasa damar amfani da hakkokinsu na kundin tsarin mulki ba tare da fargaba ba.
Ya kuma bukaci masu kada kuri’a su yi watsi da masu kokarin haddasa tashin hankali, su fito cikin lumana domin kada kuri’unsu.
Ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar kare masu kada kuri’a da tabbatar da zaman lafiya a duk tsawon lokacin zabe.
Shugaba Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su mallaki katin zabe na dindindin (PVC) tare da kula da shi, inda ya bayyana katin a matsayin wata muhimmiyar hanya ta tantance makomar siyasa da tattalin arzikin kasar.
Ya nemi yan Najeriya su mallaki PVC
Bola Tinubu ya ce:
“Shin kuna da katunan zabe? Kuna da PVC? Wannan ce makaminku, shi ne makaminku na samun ci gaba, wannan ce taswirar hanyarku.
“Ku yi amfani da shi yadda ya kamata, ku yi amfani da shi wajen zabar APC. Kada ku damu da mutanen da ke kokarin haddasa tashin hankali. Za mu kula da ku. Za a gudanar da zabe cikin zaman lafiya. Ku fito ku kada kuri’a.”
Tabbacin da Tinubu ya bayar ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan rahotannin tashin hankalin siyasa a wasu sassan kasar, yayin da jam’iyyun siyasa ke kara kaimi wajen yakin neman zabe gabanin babban zaben 2027.
Tinubu ya tabbatr da cewa gwamnatinsa za ta samar da tsaro a lokacin zabe domin tabbatar da cewa kowane dan Najeriya da ya cancanta ya ka kuri'a cikin kwanciyar hankali.
Tinubu ya yi tir da karuwar rikicin siyasa
Kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da karuwar tashe-l tashen hankula a harkokin siyasa a sassan Najeriya.
Tinubu ya ce ya kamata yakin neman zabe ya mayar da hankali kan manufofi da musayar ra'ayoyin da za su inganta rayuwar jama'a da ci gaban kasa maimakon tashe-tashen hankula.
Asali: Legit.ng

