Sojoji Sun Yi Artabu da Tsagerun 'Yan Bindiga, an Ceto Mata bayan Zubar da Jini

Sojoji Sun Yi Artabu da Tsagerun 'Yan Bindiga, an Ceto Mata bayan Zubar da Jini

  • Dakarun Sojin Najeriya ƙarƙashin Operation Fansan Yamma sun samu nasarar ceto mutum 27 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Sabuwa da ke Jihar Katsina
  • Rundunar ta gudanar da wannan samame ne ta hanyar dakarun birgediya ta 17 bayan samun kira na gaggawa daga al'ummar ƙauyen Gamji da misalin ƙarfe 12:25 na rana
  • Bayanai daga majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa sojojin sun garzaya yankin, amma 'yan ta'addan sun riga sun tsere da mutanen zuwa cikin daji kafin isowarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Sojojin Najeriya sun yi artabu mai tsanani da tsagerun 'yan bindiga a Jihar Katsina, inda suka sami nasarar ceto dukkan mutum 27 da aka sace ba tare da rasa rai a cikinsu ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro kan 2027, ya aika sako ga Atiku da sauransu

Bayan samun kiran gaggawa daga al'ummar Gamji, sojojin sun buƙaci amfani da dabarun gano hanyar da 'yan ta'addan suka bi ta ƙauyen Gangare zuwa ƙauyen Kamba, inda suka ci karo da su da misalin ƙarfe 6:05 na yamma.

Mutanen da sojoji suka ceto a Katsina
Matan da sojoji suka ceto a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa dakarun sojin sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan ta amfani da manyan makamai, wanda hakan ya tilasta musu watsar da mutanen da suka sace sannan suka tsere cikin daji.

Adadin mutanen da aka ceto

Binciken da aka gudanar a yankin bayan artabun ya kai ga ceto dukkan mutum 27, waɗanda suka ƙunshi maza 15 da mata 12, har da jaririya 'yar wata shida a duniya.

Daga bisani an mika mutanen da aka ceton ga mai garin Gamji, Alhaji Falalu Suleiman, bayan gudanar da binciken farko na lafiyarsu.

Ya rubuta cewa:

"Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa babu wani soja da ya samu rauni ko ya rasa rai a yayin gudanar da samamen, yayin da ba a gama tabbatar da adadin 'yan ta'addan da aka kashe ko suka samu rauni ba."

An tsaurara tsaro a yankin

Majiyoyin sun ƙara da cewa sojojin na ci gaba da kai komo da shawagi a dukkan faɗin yankin domin hana gudanar da dukkan ayyukan assha da hana 'yan ta'addan sakewa.

Kara karanta wannan

Samaila Kaigama ya fara fuskantar hukunci kan zargin taimaka wa 'yan ta'adda a Najeriya

An ce irin wannan nasara tana nuna muhimmancin samar da bayanan sirri a kan lokaci daga al'ummomi tare da gaggauta ɗaukar mataki na soji wajen yaƙi da garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma.

Rahoton ya ce:

"Irin wannan nasarar tana sake jaddada muhimmancin samun bayanan sirri akan lokaci daga al'ummar yankin da kuma gaggauta maida martani daga sojoji wajen yaƙi da sace mutane da sauran barazanar tsaro."
Taswirar jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Tinubu ya gana da sojoji

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci taron Hukumar Tsaro ta Ƙasa (NSC) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis, domin tattauna kan tsaron zaɓen shekarar 2027.

Taron, wanda ya ɗauki tsawon sa'o'i biyar a ofishin shugaban ƙasa, ya sami halartar Nuhu Ribadu, Janar Christopher Musa, Ministan Yan Sanda, Ibrahim Gaidam, da Babban Hafsan Tsaro Janar Olufemi Oluyede.

Sauran waɗanda suka halarta sun ƙunshi shugabannin sojin ƙasa, na ruwa, na sama, Babban Darakta na DSS, Adeola Ajayi, Babban Darakta na NIA, Mohammed Mohammed da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng