Jami’an tsaro sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a Zamfara a ranar idi

Jami’an tsaro sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a Zamfara a ranar idi

  • Dakarun ‘Yan Sandan jihar Zamfara sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su
  • Jami’an tsaro sun ce sun kubutar da wadannan Bayin Allah ne a cikin garin Maru
  • Wasu daga cikin mutanen da aka kubutar ba su da lafiya, sun gagara zuwa Gusau

Rundunar ‘yan sanda na jihar Zamfara, ta ce sun ceto mutane 100 da aka yi gaba da su a garin Dansadau da ke cikin karamar hukumar Maru.

Daily Trust ta rahoto cewa wadannan mutanen sun shafe kwanaki kusan 40 a hannun ‘yan bindiga kafin a ceto su a yau, 20 ga watan Yuli, 2021.

Tubabbun ‘yan bindiga ne su ka sa baki, a fito da wadannan Bayin Allah, bayan gwamnatin jihar Zamfara ta jagoranci wani zaman sulhu da aka yi.

KU KARANTA: Igboho ya shiga hannu, an damke shi ya na shirin zuwa Jamus

An boye mutanen da aka sace a dajin Kabaru

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Zamfara, Mohammed Shehu, ya shaida wa BBC Hausa cewa an tsare wadannan mutanen a dajin Kabaru.

“Ceton ya na cikin kokarin da jami’an tsaro su ke yi domin su kare rayuka da dukiyar al’umma."

Jaridar ta rahoto SP Mohammed Shehu ya na cewa tun da aka dauke wadannan mutanen, jami’an ‘yan sanda suka shiga neman inda za a iya gano su.

“Tun da aka dauke su, jami’an ‘yan sanda suka hada-kai da sauran jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin a tabbatar da zaman lafiya."
Jami’an tsaro sun ceto mutane
Wadanda aka sace Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan binndiga sun sace wani Likita a jihar Kogi

Ana zargin miyagun ‘yan bindiga sun dauke wadannan mutane a ranar 8 ga watan Yuni, aka boye su, sai yau ne aka ci sa’a suka samu ‘yancin kansu.

“Shirin ya dauki lokaci domin za a ceto mutane rututu ne. Akwai bukatar mu yi hattara domin gudun mu hargitsa komai, mun gode wa Allah, an dace.”

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

“Mutum 80 su ke hannun jam’an tsaro, ragowar 20 din sun gagara zuwa Gusau, ba su da lafiya, sai mu ka mika su ga ‘yanuwansu, su kula da su.”

Idan za ku tuna akalla mutane takwas da su ke tafiya a jirgin ruwa mai daukar fasinjoji ne aka sace a kan hanyar Kula-Abonrma a jihar Ribas kwanaki.

Wasu da ake zargin 'yan fashin jirgi ne sun sace matafiyan a kwanaki, a cewar shugaban kungiyar ma'aikatan jiragen ruwa na kasa, Jonah Jumbo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel