Ku rage kudin 'Data': Hukumar NCC ga kamfanonin sadarwa

Ku rage kudin 'Data': Hukumar NCC ga kamfanonin sadarwa

Hukumar sadarwan Najeriya a karshen makon da ya gabata ta yi kira ga kamfanonin sadarwa su rage kudin katin shiga yanar gizo da akafi sani da 'Data' saboda su ma an rage musu kudin lasisin birne wayoyinsu a jihohin Najeriya

Shugaba hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta, ya bayyana hakan yayainda yake jawabi ga mahalartan taron yanar gizon majalisar masu amfani da layukan sadarwa, a hedkwatar NCC dake Abuja, The Nation ta ruwaito.

Danbatta ya ce dubi ga irin hobbasan da gwamnatin Najeriya tayi na ganin cewa an ragewa kamfanonin sadarwan kudin lasisin birne wayoyinsu a jihohi zuwa kasa da N145 ga mita yayinda wasu jihohi suka yafe kudin gaba daya, ya zama wajibi su dan yunkura domin nuna godiya .

"Hukumar na sa ran cewa dubi da ragin kudin lasisin birne wayoyin da aka samu, wanda zai rage kudin da kamfanonin sadarwa zasu rika kashewa, ya kamata su nuna godiya ta hanyar rage kudin abubuwa musamman 'data' ga yan Najeriya," Ya ce

Danbatta ya kara da cewa taron mai taken: Tasirin COVID19 kan ingancin ayyukan sadarwa, ya duba yadda annoba ke juya lamura da kuma umurnin da gwamnatin tarayya ta bada na ganin an takaita yaduwa.

Ku rage kudin 'Data': Hukumar NCC ga kamfanonin sadarwa
Ku rage kudin 'Data': Hukumar NCC ga kamfanonin sadarwa
Asali: UGC

KU KARANTA: An nemi manoma 3,383 an rasa bayan sun karbi bashin CBN N364m

Tun hawar Dakta Isa Ali Pantami kujeran Ministan sadarwan Najeriya a shekarar 2019, ya yi kira ga kamfanonin sadarwa su rage gudun barewan da 'Data' ke yi sakamakon kukan da yan NAjeriya keyi a lokacin.

Bayan tsokacinsa, yan Najeriya sun bayyana samun sauki wajen yadda 'data' ke saurin karewa.

Amma duk da haka, akwai sauran bukatan rage kudin farashin musamman yanzu da annobar COVID-19 ta shafi tattalin arzikin mutane da kasa baki daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel