Lokaci Ya Yi: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Rasu, An Dauke Gawarsa daga Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- An kai gawar tsohon shugaban PDP a Jihar Edo, Cif Dan Orbih, zuwa garinsu na Ogbonna bayan dauko ta daga Abuja domin birne shi
- Gwamna Monday Okpebholo ya bayyana rasuwar Orbih a matsayin babban rashi ga Jihar Edo da ma Najeriya baki daya
- Fasto Osagie Ize-Iyamu ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai karamci da tausayi da ya taimaka wa mutane da dama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo, Nigeria - An kai gawar tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Edo, Cif Dan Orbih, zuwa garinsu na Ogbonna da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Tsakiya bayan dauko ta daga Abuja domin birne shi.
Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran za a birne Orbih bayan gudanar da ibadar coci a garinsu da ke Edo.

Source: Facebook
Gawar Dan Orbih ta isa jihar Edo
The Nation ta ruwaito cewa gawar marigayin ta iso birnin Benin daga Abuja a ranar Juma’a, inda Gwamna Monday Okpebholo da wasu manyan ’yan siyasa a jihar suka tarbe ta.
Gwamnan, ’yan uwa, abokai, abokan siyasa da jami’an gwamnati sun raka gawar daga filin jirgin sama zuwa gidan marigayin da ke yankin GRA a birnin Benin, inda aka gudanar da taƙaitaccen bikin nuna gawar kafin a kai ta wurin jana’iza.
Gwamnan Edo ya yi ta'aziyya
Da yake jawabi a wajen bikin, Hwamna Okpebholo ya bayyana rasuwar Orbih a matsayin babban rashi ga Jihar Edo, inda ya ce marigayin ya wuce abokin siyasa a wurinsa.
“Ya kasance ɗan’uwa a gare ni. A irin wannan lokaci, lokacin da yake da wuya a jure rashin wanda muke ƙauna, abin da za mu iya yi shi ne komawa ga Allah domin samun ta’aziyya da ƙarfi.
“Ina addu’ar Allah Ya ba mu baki ɗaya ƙarfin zuciya da juriyar jure wannan babban rashi.
“Ina kuma addu’ar Ubangiji Ya kiyaye iyalansa, Ya ƙarfafa su a wannan lokaci mai wahala, Ya kuma ba su ikon ci gaba da rayuwa,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Bayan rage farashi, Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan yiwuwar dawo da tallafin fetur kafin 2027
Yadda aka yi juyayin rasuwar Dan Orbih
Limamin da ya jagoranci ibadar, Rabaran Palmer Ikponmwosa, ya bayyana Orbih a matsayin fitaccen mutum a siyasar Edo, ƙwararren mai tsara dabarun siyasa, shugaba kuma wanda ke da tasiri wajen zaɓar waɗanda za su samu mukamai.

Source: Facebook
Wani jigo a jam’iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, shi ma ya yi ta’aziyyar marigayin, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai karamci da tausayi wanda ya taimaka wa mutane da dama.
“Zan iya tunanin irin yadda duk waɗanda suka amfana da karamcinsa suke ji bayan rasuwarsa,” in ji shi.
Masanin sadarwa a Najeriya ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa shahararren masanin sadarwa kuma jigo a fannin yaɗa labarai da sadarwa a Najeriya, Farfesa Idowu Akanbi Sobowale, ya rasu yana da shekara 85.
An bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’ummar fannin sadarwa, musamman mambobin kungiyar masa da kwararrun sadarwa ta Najeriya.
Asali: Legit.ng
