Gwamna Ya Kaɗu da Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Gwamna Ya Kaɗu da Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Gwamna Ahmadu Fintiri ya bayyana kaduwarsa kan rashin shugaban ƙaramar hukuma da aka yi a jihar Adamawa
  • Dr. Yahaya Saidu, shugaban karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, ya rasu a daren Asabar, 10 ga Oktoba, 2026
  • Dan majalisar tarayya mai wakiltar Fufore da Song, Aliyu Boya Wakili, ya yi alhinin rasuwar Saidu, tare da yi wa iyalansa addu'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa – Dr. Yahaya Saidu, shugaban karamar hukumar Fufore da ke jihar Adamawa, ya rasu a daren Asabar, 10 ga Oktoba, 2026.

Majiyoyi sun tabbatar da labarin rasuwarsa ce lamarin da ya jawo jimami da alhini a tsakanin al'ummar Fufore da jihar Adamawa.

Fintiri ya yi jimamin rashin shugaban ƙaramar hukuma
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa. Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri.
Source: Twitter

Gwamna ya yi alhinin mutuwa ciyaman a Adamawa

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya nuna alhininsa kan rashin da aka yi wanda ya wallafa a shafin X a yau Asabar 10 ga watan Oktobar shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu ya 'kunyata' Bashir Ahmad a wani taron APC, an yaɗa bidiyon APC

Manyan jami'an gwamnati sun bayyana alhininsu kan rasuwar shugaban karamar hukumar, tare da mika sakonnin ta'aziyya ga iyalansa da al'ummar yankin.

Fintiri ya ce:

"Na shiga matukar kaduwa da bakin ciki sakamakon rasuwar bazata ta shugaban karamar hukumar Fufore, Dr. Yahaya Saidu. Ma'aikacin gwamnati ne mai tawali'u, kuma rashinsa ya girgiza al'ummar Adamawa.
"Ina tare da iyalansa da al'ummar Fufore a wannan lokaci na jimami, tare da yi musu addu'a. Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi Aljannatul Firdaus."

Dan Majalisar Tarayya Ya Yi Alhinin Rasuwarsa

Hon. Barr. Aliyu Boya Wakili, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Fufore da Song a Majalisar Wakilai, shi ma ya yi alhinin rasuwar shugaban karamar hukumar.

A cikin sakon ta'aziyyarsa, Wakili ya bayyana rasuwar Saidu a matsayin babban rashi ga al'ummar yankin, tare da rokon Allah Ya gafarta masa kura-kuransa.

Ya kuma yi addu'ar Allah Ya karbi kyawawan ayyukansa, Ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus.

Kara karanta wannan

Shugaban karamar hukuma ya rasu a Adamawa, wata 3 da rantsar da shi

Haka kuma, ya roki Allah Ya bai wa iyalan mamacin, abokansa, abokan aikinsa da daukacin al'ummar Fufore hakuri da juriya wajen jure wannan babban rashi.

An yi rashin shugaban karamar hukuma a Adamawa
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da marigayi Dr. Yahaya Saidu. Hoto: @GovernorAUF.
Source: Twitter

Yaushe za a yi sallar jana'izar marigayin?

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a sanar da lokacin gudanar da jana'izar marigayin ba yayin yan uwa da abokan arziki ke ci gaba da jimamin rashinsa.

Ana sa ran iyalansa za su fitar da sanarwar jana'izar nan gaba domin bayyana lokacin sallar jana'izar marigayin.

Babban malamin Musulunci ya rasu a Adamawa

An ji cewa an sanar da rasuwar wani malamin Musulunci a jihar wanda ya bayar da gudummawa ga addini matuka kafin rasuwarsa a wannan lokaci.

An tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a safiyar Juma’a, 9 ga Oktobar shekarar 2026 da muke ciki, bayan gajeriyar rashin lafiya da ya yi fama da ita.

An a gudanar da sallar jana’izarsa a yau Juma’a, a Masallacin Dodore da ke Yola, da ƙarfe 4:00 na yamma bayan sallar La’asar a jiya Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.