Mutuwa Ta Kara Girgiza Najeriya, Fitaccen Masanin Sadarwa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Shahararren masanin sadarwa kuma jigo a fannin yaɗa labarai da sadarwa a Najeriya, Farfesa Idowu Akanbi Sobowale, ya rasu yana da shekara 85
- Wani ɗan uwansa, Akinniyi Sowunmi, ya sanar da rasuwar a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, 2026
- Sobowale ya yi fice a fannin aikin jarida da ilimin sadarwa, inda ya taka rawa wajen kafa Jami’ar Jihar Legas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun, Nigeria - Shahararren masanin sadarwa kuma gogaggen memba a harkar yaɗa labarai da sadarwa a Najeriya, Farfesa Idowu Akanbi Sobowale, ya riga mu gidan gskiya.
An tattaro cewa Farfesan ya rasu ne ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban 2026 yana fa shekaru 85 da haihuwa.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito vewa wani ɗan uwansa, Akinniyi Sowunmi, ne ya sanar da rasuwar a cikin wata sanarwa mai taken “Transition to Glory” a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take
Farfesa Sobowale ya mutu
Sowunmi ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’ummar fannin sadarwa, musamman mambobin kungiyar masa da kwararrun sadarwa ta Najeriya.
Ya rubuta cewa:
“Wannan rana ce mai matuƙar baƙin ciki a gare mu a al’ummar fannin sadarwa ta Najeriya, musamman a gare mu a yan kungiyar Association of Communication Scholars & Professionals in Nigeria.
"Ubanmu, Pa Deacon Farfesa Idowu Akanbi Sobowale, OON, mai shekara 85, ya koma ga mahaliccinsa a safiyar yau, 8 ga Oktoba, 2026. Iyalansa za su sanar da cikakken bayani kan shirye-shiryen jana’izarsa nan ba da jimawa ba.”
Rayuwar Farfesa Sobowale
An haifi Farfesa Idowu Akanbi Sobowale ranar 4 ga Janairu, 1941, a Ashipa da ke kusa da Abeokuta a jihar Ogun, mahaifinsa manomi ne yayin da mahaifiyar ke sana’ar kasuwanci.
A cikin shekaru 12 na farko na rayuwarsa, ya yi aikin noma da kuma koyon aikin gyaran motoci. Sai a watan Janairun 1954 ne ya fara shiga aji a makaranta.
Daga baya ya halarci Jami’ar Legas, inda ya samu Diploma da digirin BA (HONS) a fannin sadarwar jama’a.
A shekarar 1975, ya bar Daily Times ya koma Jami’ar Legas a matsayin mataimakin malami a Cibiyar Sadarwar Jama’a.
Bayan shekara guda, ya tafi jami'ar Syracuse da ke Amurka domin karatun digiri na biyu, amma ya dawo a shekarar 1978 da digirin PhD, inda ya ƙware a fannin aikin jarida na kimiyya da ingantaccen bincike.

Source: Facebook
Ya kafa tarihi a jami'ar LASU
A shekarar 1983, Jami’ar Jihar Legas ta naɗa shi Farfesan Aikin Jarida, jami’ar da ya taimaka wajen kafawa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ayyukan farko da Farfesa Sobowale ya yi, da sauran gudunmawarsa, sun sa gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo ta ba shi lambar yabo ta ƙasa ta (OON) a lokacin Jamhuriyya ta Hudu.
Jigo a NADECO ya kwanta dama
Kun ji cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa National Democratic Coalition (NADECO), Cif Ralph Obioha, ya rasu yana da shekara 80.
Iyalansa sun bayyana shi a matsayin uba, miji, ɗan’uwa, kaka da aboki mai matuƙar ƙauna, sun ce ya rasu ne ranar 3 ga Oktoba, 2026
Asali: Legit.ng
