Tanko, Onnoghen, da Uwais da sauran Alkalai 15 da suka hau kujerar Alkalin Alkalai na kasa

Tanko, Onnoghen, da Uwais da sauran Alkalai 15 da suka hau kujerar Alkalin Alkalai na kasa

  • Mun kawo jerin duk wanda suka taba rike mukamin Alkalin Alkalai a Najeriya
  • Adetokunbo Ademola shi ne ya fi kowa dade wa a ofis, ya kusa shekara 15 a CJN
  • A jerin akwai irinsu Taslim Olawale Elias wanda ya yi Ministan shari’a na kasa

Nigeria - Burin duk wani babban Alkali ya zama Alkalin Alkalai na kasa. Alkalin Alkalai wanda ak fi sani da CJN shi ne shugaban bangaren shari’a na kasa.

Shugaban kasa yana zaben babban Alkalin kotun koli a matsayin shugaban Alkalai bisa shawarar NJC. Dole majalisar dattawa ta tantance shugaban Alkalan.

Sannan sai da sa hannun mafi yawan ‘yan majalisa dagoyon bayan majalisar shari’a NJC ne za a iya sauke CJN, ko kuma idan har ya cika shekara 70 a Duniya.

Kara karanta wannan

Terere: Yadda Fasto Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa

A halin yanzu Mai shari’a Ibrahim Tanko Mohammed ne yake kan wannan kujera tun 2019. Kafin yanzu ya yi aiki a kotun shari’a da kuma kotun daukaka kara.

Kafin Tanko Mohammed, Walter Nkanu Onnoghen shi ne Alkalin Alkalai. Shi ne mutumin kudu da ya rike wannan mukami a karon farko cikin shekaru 32.

Tanko, Onnoghen, da Uwais da sauran Alkalai 15 da suka hau kujerar Alkalin Alkalai na kasa
Aloma Maryam Mukhtar da Goodluck Jonathan www.thecable.ng

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Walter Onnoghen ya yi murabus, mace ta kafa tarihi a 2012

Daga baya aka tursasa wa Walter Onnoghen ya ajiye mukaminsa saboda wasu zargi da ke kansa.

Mahmud Mohammed, Dahiru Mustafa, Aloysius Katsina-Alu, Idris Kutigi, Salihu Belgore, Lawal Uwais da Mohammed Bello sun rike kujerar na shekaru 27.

A shekarar 2012 aka samu macen da ta zama CJN. Shugaban kasa na wancan lokaci, Goodluck Jonathan ya nada Aloma Maryam Mukhtar, ta sauka a 2014.

Adetokunbo Ademola, Mohammed Bello, da Muhammad Lawal Uwais sune su ka fi dade wa a ofis. Kafin Ademola, Birtaniyawa ne suka yi ta rike kujerar CJN.

Kara karanta wannan

Kwana daya bayan jefa 'dansa kurkuku, Kotun ta sake watsawa AbdulRashid Maina kasa a ido

Legit.ng Hausa ta tattaro ‘yan kasa da suka taba zama shugabannin Alkalai a tarihin Najeriya. Mun tsakuro wasu daga cikin bayanan ne daga shafin Wikepedia.

1. Ibrahim Tanko Mohammed - 2019 - yau

2. Walter Samuel N. Onnoghen - 2017 - 2019

3. Mahmud Mohammed - 2014 - 2016

4. Aloma Maryam Mukhtar - 2012 - 2014

5. Dahiru Mustafa - 2011 - 2012

6. Aloysius Iyorgyer Katsina-Alu- 2009 - 2011

7. Idris Legbo Kutigi 2007 - 2009

8. Salihu Alfa Belgore 2006 - 2007

9. Muhammad Lawal Uwais 1995 - 2006

10. Mohammed Bello - 1987 - 1995

11. Ayo Irikefe - 1985 -1987

12. George Sodeinde Sowemimo - 1983 - 1985

13. Atanda Fatai Williams - 1979 - 1983

14. Taslim Olawale Elias - 1972 – 1975

15. Adetokunbo Ademola - 1958 - 1972

Shari'a a jihar Imo?

A ranar Juma'a aka ji Gwamna Hope Uzodinma ya kafa majalisar da za ta rika kula da tituna da motoci a Imo, sannan ya hana saida giya a tashoshin mota.

Sanata Uzodinma ya naganin wannan mataki zai rage aukuwar haduran da ake yi a jihar Imo. Sai dai hakan ya jawo surutai daga wasu mutane a yankin kudu.

Kara karanta wannan

Jami’an DSS sun kama Hadimin Gwamna, mutum 2 da zargin satar kudin da aka ware wa talakawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel