Dan Siyasar Najeriya Ya Rasu Wata 3 da Rantsar da Shi a Sabuwar Kujera
- Shugaban karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, Yahya Saidu, ya rasu ranar Juma'a, wata 18 bayan mutuwar magabacinsa a kan karagar mulki
- Dan majalisar wakilai mai wakiltar Fufore/Song, Aliyu Wakili, ne ya tabbatar da rasuwar, inda ya bayyana ta a matsayin babban rashi ga al'ummar Adamawa
- Mutuwar shugabannin karamar hukumar biyu a cikin wata 18 ta jawo tsokaci daga masu sharhi kan siyasa, yayin da al'umma da abokan siyasa ke mika sakonnin ta'aziyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Adamawa – Shugaban karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, Yahya Saidu, ya rasu ranar Juma'a, kimanin wata 18 bayan rasuwar mutumin da ya gada a mukamin.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Fufore/Song, Aliyu Wakili ne ya tabbatar da rasuwar a cikin sakon ta'aziyya da ya fitar ranar Asabar.

Source: Facebook
A sakon da ya fitar a Facebook, Wakili ya bayyana mutuwar Saidu a matsayin babban rashi ga al'ummar karamar hukumar Fufore da jihar Adamawa baki daya.
Sakon ta'aziyyar dan majalisar
Hon. Aliyu Wakili ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya karbi kyawawan ayyukansa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus.
Ya kuma roki Allah Ya bai wa iyalansa, abokansa, abokan hulda da daukacin al'ummar Fufore hakuri da juriyar jure wannan babban rashi.
Mutuwar ta girgiza jama'a
Rasuwar Saidu ta sake jawo tunani a jihar, kasancewar ta zo ne wata 18 bayan mutuwar magabacinsa, Shuaibu Babas, wanda ya rasu yana kan mukami a ranar 23 ga Afrilu, 2025.
Wani mai sharhi kan siyasa a jihar, Abu-Taqiyah Zumo, ya bayyana rasuwar shugabannin karamar hukumar biyu a jere a matsayin wani lamari mai girgiza rai da kuma tunatarwa kan yadda rayuwa take wucewa.
Premium Times ta rahoto Zumo ya ce rasuwar Babas da Saidu, wadanda suka shugabanci karamar hukumar Fufore daya bayan daya, ta nuna cewa mulki da mukami ba su dawwama.

Source: Original
Ya bayyana cewa kujera da mukami na iya ci gaba da kasancewa, amma masu rike da su suna barin duniya, yana mai cewa abin da zai fi muhimmanci a karshe shi ne irin tasirin da mutum ya yi a rayuwar jama'a, ba mukamin da ya rike ba.
Ana ci gaba da ta'aziyya
Sakonnin ta'aziyya da addu'o'i na ci gaba da fitowa daga sassa daban-daban na jihar Adamawa, yayin da shugabannin al'umma, abokan siyasa da wadanda marigayin ya wakilta ke jimamin rasuwarsa.
Jama'a na kuma addu'ar Allah Ya ba iyalansa da sauran makusantansa hakuri da juriya a wannan lokaci na alhini.
An kashe Sarki a Kano
A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad, dagacin kauyen Aujarawa da ke karamar hukumar Gezawa a jihar Kano, daga gidansa da sanyin safiyar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026.
Rahotanni sun ce maharan sun isa gidan da misalin karfe 1:30 na dare, suna tafiya a kafa tare da harbe-harbe a sama kafin su kutsa cikin gidan.
Dan uwan marigayin, Muhammad Auwal, ya shaida cewa maharan sun lakada wa babban dan uwansa duka a gaban iyalansa kafin su tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Asali: Legit.ng

