Ta'aziyya mai ratsa zuciya da Tinubu ya aika wa Buhari bayan ya yi rashin dan uwa

Ta'aziyya mai ratsa zuciya da Tinubu ya aika wa Buhari bayan ya yi rashin dan uwa

A ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu ne shugaban jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari mutuwar dan uwansa, Ibrahim Dauda.

A sakon ta'aziyyar da hadimin Tinubu, Tunde Rahman ya mika ga iyalan Dauda, Gwamnan Masari, jama'ar Daura da kuma jihar Katsina baki daya, ya yi alhinin wannan babban rashin.

Idan za mu tuna, Dauda ya rasu a Daura da ke jihar Katsina bayan doguwar jinyar da yayi.

Shugaban na APC ya ce: "Ina mika ta'aziyyata ga shugaban kasa a kan mutuwar dan uwansa, Alhaji Ibrahim Dauda.

"Ina mika ta'aziyyata ga iyalan mamacin, Gwamna Aminu Masari da jama'ar garin Daura.

"Babu dadewa aka yi mutuwar wani dan uwan, sai ga wannan ta faru, tabbas hakan zai kara zafin rashin," yace.

Ta'aziyya mai ratsa zuciya da Tinubu ya aika wa Buhari bayan ya yi rashin dan uwa
Ta'aziyya mai ratsa zuciya da Tinubu ya aika wa Buhari bayan ya yi rashin dan uwa Hoto: Siverbird TV
Asali: UGC

Tinubu ya yi kira ga Buhari da iyalansa da su dauki hakuri sakamakon wannan babban rashin da suka yi.

Ya yi fatan Allah ya tausasa zukatan matarsa, 'ya'yansa da 'yan uwan sa a kan wannan babban rashin.

"Ina fatan Allah ya tallafa tare da baku karfin zuciya a wannan lokacin da kuke fama da rashin dan uwa.

"Ga mamacin, Allah ya sa kyawawan ayyukansa su bi shi, ya yafe masa zunubansa tare da saka shi a Aljannah," yace.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya gana da kwamitin yaki da annobar korona a kasa (Hotuna)

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Alhaji Tukur Jakada, mamba mai wakiltar mazabar Bakura a majalisar dokokin jihar Zamafara, ya mutu.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar Zamfa, Shamsudeen Hassan, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke magana da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Hassan ya ce Jakada ya mutu ne ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, bayan wata gajeriyar jinya.

Kafin mutuwarsa, Jakada ya kasance shugaban kwamitin harkokin kananan hukumomi da sarautu.

'Yan bindiga a jihar Katsina sun kashe shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Batsari, Abdulhamid Sani Ruma, a kauyensu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel