'Farashin Abinci da Fetur Ya Sauka a Najeriya': Minista Ya Zayyano Alheran Tinubu
- Ministan sadarwa, Mohammed Idris, ya ce sauye-sauyen da shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa sun fara haifar da ɗa mai ido a Najeriya
- Ya ce ana samun raguwar wahalhalu bayan aiwatar da manufofin gwamnati, ciki har da saukar farashin kayan abinci da na man fetur
- Ministan ya bukaci shugabannin addini su yi addu’o’i tare da fahimtar da mabiyansu a muhimancin zaman lafiya da ci gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan sadarwa da wayar da kan 'yan kasa, Mohammed Idris, ya ba da tabbacin cewa tarihi zai yi wa shugaba Bola Tinubu adalci, duba da jajircewarsa wajen cigaban Najeriya.
A cewar ministan, Tinubu yana tafiyar da mulkinsa da kishin kasa da kuma cikakken tunani na sauke nauyin da Allah ya dora masa.

Asali: Twitter
Idris ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na ministoci da aka gudanar a Abuja, a ranar Alhamis, 13 ga Maris, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu saukin farashin abinci da fetur
Mohammed Idris ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa suna da matukar muhimmanci wajen daidaita kasar a dogon zango.
Ya ce, duk da cewa matakan suna da wahala a yanzu, alamu na nuna cewa sun fara haifar da sakamako mai kyau a fannoni da dama.
"Mun tsallake mawuyacin hali, kuma wahalhalun da ke tattare da sauye-sauyen suna raguwa yayin da sakamakon ke fara bayyana," in ji shi.
Ministan ya kara da cewa, yanzu ana samun raguwar farashin abinci, daidaiton darajar Naira a kasuwar musaya, da saukar farashin man fetur, wanda ke nuna ingancin manufofin gwamnati.
'A kara hakuri' - Ministan sadarwa
Ya amince da cewa sauye-sauye masu muhimmanci sau da yawa suna fuskantar adawa saboda wahalhalun da ke tattare da su, amma ya jaddada cewa suna da matukar amfani ga cigaban kasa.
"A duk duniya, tarihi ya nuna cewa duk wani sauyi mai ma’ana yana bukatar hakuri, sadaukarwa, da hangen nesa domin samun cigaba mai dorewa," in ji ministan.
Ya bayyana cewa wahalhalun da ake fuskanta a halin yanzu wata sadaukarwa ce da 'yan kasa za su yi domin samun ingantacciyar makoma ta tsawon lokaci.
Gwamnati ta sake tausasar zuciyar 'yan Najeriya

Asali: Twitter
Idris ya gode wa ‘yan Najeriya bisa hakuri da goyon bayan da suke bai wa gwamnati, yana mai kira ga shugabannin addini da su ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya da tsaron kasa.
"Ina kira ga malamai Musulmi da Kiristoci su yi amfani da lokutan Ramadan da Azumin Lent wajen addu’o’i ga zaman lafiya da cigaban Najeriya,"
- in ji Idris.
A taron, ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, da ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa, sun bayyana nasarorin da ma’aikatunsu suka samu a kokarin gwamnatin Tinubu na kawo ci gaba a kasar.
Sun jaddada cewa gwamnatin na aiki tukuru don tabbatar da cewa manufofinta sun inganta rayuwar ‘yan Najeriya ta hanyar daukar matakan da suka dace domin cigaban kasa.
Farashin fetur zai ci gaba da sauka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, masanin tattalin arziki, Bismarck Rewane, ya bayyana cewa farashin man fetur zai ci gaba da raguwa har zuwa Yuni 2025.
Ya yi wannan bayani ne bayan rage farashin fetur da kamfanin Dangote da NNPCL suka yi, wanda zai saukaka wa ‘yan Najeriya wahalhalu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng