Batanci ga Annabi: Majalisar shari'ar Musulunci ta bukaci Ganduje ya sa hannu don rataye Sharif

Batanci ga Annabi: Majalisar shari'ar Musulunci ta bukaci Ganduje ya sa hannu don rataye Sharif

- Majalisar shari’a ta Najeriya ta bukaci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya aiwatar da hukuncin mutumin da ya yi batanci ga Annabi

- Majalisar ta ce hukuncin da aka zartar na kashe wani mawaki mai shekaru 22 kan zagin Annabi Muhammadu lamari ne na addini tsantsa

- Ga fusatattun al’umman da suke ba Musulmi ba, majalisar ta ce hukuncin na a kan tafarkin dokar kasar ne

An bukaci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da ya sanya hannu a kan hukuncin kisa da aka yanke wa Aminu Sharif, wani mawaki mai shekaru 22 ta hanyar rataya kan zargin batanci ga Annabi.

Rokon na kunshe ne a cikin wani jawabi daga majalisar kolin shari’a a Najeriya (SCSN) ta hannun sakatarenta, Nafi’u Baba-Ahmed, a ranar Talata, 18 ga watan Agusta.

Legit.ng ta tuna cewa lamarin ya haddasa kace nace sannan ya sa Wata babbar kotun shari’a da ke Kano ta yanke wa Sharif hukuncin kisa ta hanyar rataya kan zargin zagin Annabi Muhammad.

A wani hukunci da Khadi Aliyu Muhammad Kano na kotun shari’a da ke zama a Hausawa Filin Hockey ya zartar, an kama mawakin da laifin batanci tare da hukuncin cewa ya rera waka wacce baitukanta ke batanci ga Annabi.

Batanci ga Annabi: Majalisar shari'ar Musulunci ta bukaci Ganduje ya sa hannu don rataye Sharif
Batanci ga Annabi: Majalisar shari'ar Musulunci ta bukaci Ganduje ya sa hannu don rataye Sharif Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

An kuma tattaro cewa mawakin ya watsa wakar batancin zuwa ga kafar zumunta ya WhatsApp a watan Maris din 2020.

Ana ta sharhi daban-daban kan hukuncin kotun Musuluncin yayinda wasu ‘yan Najeriya ke kallon hukuncin a matsayin wanda ya yi tsanani.

Sun yi al’ajabin dalilin da yasa ba a yanke wa ‘yan Boko Haram da aka kama irin wannan hukuncin ba.

Sai dai SCSN, ta jinjinawa hukuncin sannan tana so gwamnatin jihar Kano ta aiwatar da kisan mawakin.

Kiran da kungiyoyin da ake kira da masu kare hakkin dan Adam ke yi na son a yi wa mai laifin afuwa kada ya hana gwamnatin jihar aiwatar da abunda ya dace.

“Wannan lamari na addinin Islama ne tsantsa kuma daidai da tsarin addini, al’ada da muradin mutane ba wai na Kano ba kadai, na mafi rinjayen ‘yan Najeriya wadanda suka kasance Musulmi.”

Kungiyar ta bukaci Musulmai da su kula da irin furucin da za su yi kan addinin Islama da annabinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel