'Yan sanda sun kama tsohon ɗan majalisa da mutane 2 bisa zargin harkar ƙungiyar asiri

'Yan sanda sun kama tsohon ɗan majalisa da mutane 2 bisa zargin harkar ƙungiyar asiri

  • ‘Yan sanda sun kama tsohon dan majalisar jihar Ogun da wasu mutane 2 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne
  • Hakan ya biyo bayan korafin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Ijebu ta arewa II, Oludare Kadiri ya kai mu su
  • Kadiri ya kai korafin ne yana zargin su da yin kulle-kullen kai masa farmaki da kuma yunkurin halaka shi

Jihar Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta samu nasarar kama wani tsohon dan majalisar jihar, Mr Joseph Adegbesan da wasu mutane 2 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, hakan ya biyo bayan korafin su da Oludare Kadiri, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ijebu ta arewa II ya kai wa rundunar.

'Yan sanda sun kama tsohon ɗan majalisa da mutane 2 bisa zargin harkar ƙungiyar asiri
Jami'an 'yan sandan Nigeria. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Ana zargin su da shiga hakkin al’umma, kai farmaki ga rayuwar jama’a da mallakar miyagun makamai ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Kwana 5 da mutuwar Mailafia, ba bu saƙon ta’aziyya daga Buhari da El-Rufai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuni aka zarce da wadanda ake zargi zuwa jihar Legas

Jami’an bincike na sirri, IRT na hedkwatar Abuja sun wuce da dan majalisar kuma sun zarce da shi jihar Legas tare da wasu mutane 2, Muibi Olufodun da wani Samson.

Wani dan jam’iyyar APC na yankin ya sanar da Premium times cewa sauran wadanda aka so kama wa sun ranta a na kare.

Kamar yadda mutumin wanda ba ya so a bayyana sunan sa ya ce:

“Tabbas rundunar ‘yan sandan ta zo yau ta kama Hon. Adegbesan. Sun kama shi a Awa ne (wani gari dake karamar hukumar Ijebu ta arewa da ke jihar Osun).”
“An kama Muibi a Ago-Iwoye. Kuma an kama duk sauran wadanda ake zargi. Mun gano cewa ‘yan sandan duk ‘yan rundunar IG ne.”

Kara karanta wannan

Kano: Hotunan ɓarayin waya uku da aka kama a bayan sun kashe wani sun ƙwace wayansa

Sifeta janar da kan shi ya bayar da umarnin kama su

An gano cewa sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali ne ya umarci mataimakin sa dake kula da FIB don ya yi gaggawar daukar mataki akan korafin da lauyan Kadiri, Oludare Adajare ya kai yana zargin suna yunkurin kai wa rayuwar wanda yake karewa farmaki.

Abimbola Oyeyemu, kakakin rundunar na jihar Ogun ya tabbatar da kamen amma ya kara da cewa rundunar IRT ne kadai za su iya bayanai dalla-dalla.

Kadiri, wanda shine dan majalisa mai wakiltar mazabar Ijebu ta arewa II dake jihar Ogun ya zargi Adegbesan, wanda ya gaji kujerar sa da daukar nauyin wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne don sun kai masa farmaki kuma su halaka shi.

Wakilin Premium Times ya ga takardar korafin inda yace wasu daga cikin wadanda ake zargin sun bayyana yadda su ka halaka dalibai 2 na jami’ar Olabisi Onabanjo da ke Ago-Iwoye.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure

A wani labarin daban, wani tsoho mai shekaru 84, Peter Oyuk ya sha mamakin yadda matan sa 2 suka sake aure bayan ya yi tafiya tsawon shekaru 47.

Kamar yadda LIB ta ruwaito daga The Standard, mutumin ya bar kauyen Makale dake Malava bangaren Kakamega a shekarar 1974 lokacin yana da shekaru 37.

Ya sanar da iyalan sa cewa ya tafi neman arziki don tallafa wa matan sa 2 da yaran sa 5 duk da dai bai sanar da su lokacin da zai dawo ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel